BBC Hausa of Monday, 28 March 2022
Source: BBC
A yayin da ake tsaka da barkewar annobar korona, wani mawaki da ke zaune a Birtaniya ya hau jirgi zuwa Ghana domin hada gwiwa da wani yaro dan makaranta don yin wata waka wadda ke nuna sabon salon waka a Afirka. Wakar, mai suna Sore, da Yaw Tog, matashi mai shekara da Stormzy suka yi ta karbu sosai a YouTube inda fiye da mutum miliyan shida suka kalle ta.
Salon wakar Asakaa na Ghana shi ne ke tashe yanzu a Afirka kuma tana fatan zai samu karbuwa irin wadda salon wakar Afrobeats na 'yan Najeriya da salon wakar amapiano na Afirka ta Kudu suka samu a duniya.
Salon wakar na Asakaa ya hada da irin wakokin Ghana da wani bangare na salon wakar gambara da ake yi a Amurka da kuma amfani da karin-harshen Twi.
Daya daga cikin masu son irin wannan salo na waka shi ne, marigari Virgil Abloh, dan kasar Ghana mazaunin birnin Chicago, a cewar mawaki Kwaku DMC.
Lokacin da darakta a kamfanin yin tufafi na Louis Vuitton kuma makusancin Kanye West ya ga bidiyon salon wakar asakaa mai suna Suzy a shafukan sada zumunta, ya wallafa shi a shafinsa na Instagram sannan ya ja hankalin Kwakwu DMC.
"Na tashi da safe tare da yin karo da sakonnin, sakonni da dama suka shigo mun, kamar me ke faruwa. Shin an yi mun kutse ne ko wai abu daban?" yana iya tunawa. "Sai na garzaya akwatin sako na sai kawai aga ashe Virgil ta ambato suna na."
Kwaku DMC shi ma ya bi Abhol, wanda ya fadamasa cewa wakar tayi "wuta" kuma wai ya yi farin ciki ganin matashin ɗan Ghana da irin wannan wakar". Kuma ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen taimakawa wakar da soma aiko mun da tufafi da takalma.
Mawaki da ke tasowa Jay Bahd nada yaƙinin asakaa na daya daga cikin matasa da ke tasowa da za su bada mamaki daga Ghana, kuma wannan fata ba boyayya ba ne.
Manhajar sauraron wakoki da ke mayar da hankali kan kasuwar Afrika, Boomplay, ya ce wakokin da ake nunawa kauna na Yow Tog da Jay Bahd na cikin wakoki 20 da aka fi saurara.
Wakar ta su ta karade yakuna da dama kama daga Amurka da Burtaiya da Jamus
Sai dai amfani da yaransu shi ne abin da ya sa wakarsa ta yi fice kuma ta bambanta.
Sunan kadai abu ne da mutane ke nunawa soyayya a duniyar wakoki.
Kalmar "magana da harshen Twi shi ne "kasa", kuma asakaa ya yi amfani da ita sosai.
Makadi kuma mai shirya waka Rabby Jones shi ya zo da kalmar. Yana tukin mota cikin tsakiyar dare tare da wasu mawaka daga Kumasi babban birnin Ghana, na yankin Ashanti.
"Mun saki kida irin na zamani, kuma Jay Bahd ya kasance wanda yake gambara. Na yi ihu na ce: Asakaa. Nan danan abin ya zo mun kuma muka ci gaba a haka, a cewarsa.
Duk da cewa asalinsa ba mawakin asakaa ba ne, amma ya kan bambanta kansa da salon kida Ghana da Burtaniya,.
An sake haifo asakaa a yankunan makwaftan Kumasi kuma abin ya karade ko ina a kasar.
Duk da cewa wannan salon wakar ya karbu a yammacin Ghana, wannan abu ne da matasa mawaka da masu shirya wakoki a Kumasi ke kokarin sake karfafawa, suna tabo yada sautin kidan ya samu cigaba tun daga 2020.
"Ba su da masaniya sosai kan abin da ya kamata su yi," a cewar mawaki gambara O'Kenneth.
"Amma duniya ta karɓi wannan salon wakar da kida a cewar O'Kenneth, wanda ya soma daukar hankali har a shafukan sada zumunta saboda litattafansa da hadin-gwiwar da ya da Kumerica a Agustan 2020.
Duk da cewa muryarsa ta bambanta a zahiri, a lasifika murya na da tausasawa.
Yana kaunar kasarsa, Ghana, amma ya fi samun karbuwa a Turai, kuma yana samun habaka a duniya.
Tsattsauran yanayin al'ummar Kumasi na nuna cewa har yanzu akwai mutanen da ba su rungumi akidar asakaa ba.
O'Kenneth na fahimci cewa akasarin masoyansa sun fito ne daga yammaci.