BBC Hausa of Wednesday, 15 March 2023
Source: BBC
Real Madrid za ta kara da Liverpool ranar Laraba a wasa na biyu a Champions League, zagayen 'yan 16 a Santiago Bernabeu.
Ranar 21 ga watan Fabrairu, Real ta ci Liverpool 5-2 a wasan farko a Anfield a gasar zakarun Turai ta bana.
Liverpool ce ta fara zura kwallo biyu a raga ta hannun Darwin Nunez da Mohamed Salah a Anfield.
Daga baya Real ta ci biyar ta hannun Vinicius Junior da ya zura biyu a raga da Eder Militao mai daya da kuma Karim Benzema da shima ya ci biyu.
A bara Real ta doke Liverpool 1-0 a Faransa ta dauki Champions League na 14 jimilla, karo na biyu da ta dauki kofin a kan Liverpool a tarihi.
A kakar 2017/18, Real ta ci Liverpool 3-1 a Lisbon ta lashe Champions League.
Sun yi wasa 10 a tsakaninsu, Real ta ci shida, Liverpool ta yi nasara a uku da canjaras daya.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki tara tsakaninta da Barcelona ta biyu a bana.
Ita kuwa Liverpool tana ta shida a Premier League da maki 42, bayan da Arsenal ke jan ragama mai maki 66, bayan wasan mako na 27.
Tuni Carlos Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da zai fuskanci Liverpool a Santiago Bernabeu.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin and Luis López.
Masu saron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger and Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni and D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano and Álvaro.
Jerin wasa da aka buga tsakanin kungiyoyin biyu:
2022/2023 Champions League