You are here: HomeAfricaBBC2023 04 10Article 1746950

BBC Hausa of Monday, 10 April 2023

    

Source: BBC

Abin da kuke son sani kan wasan Barca da Girona

Yan wasan Barcelona Yan wasan Barcelona

Barcelona za ta kara da Girona a La Liga wasan mako na 28 da za su fafata ranar Litinin a Camp Nou.

Barcelona za ta buga wasan bayan da Real Madrid ta fitar da ita a Copa del Rey, bayan doke ta 4-0 a Camp Nou.

To sai dai Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu mai rike da kofin bara.

Girona mai maki 34 tana ta 11 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, bayan karawa 27.

Girona birni ne na kwararrun masu wasan tseren kekuna da hada fina-finai - birnin ya dade a fannin tamaula a rukuni na biyu da na uku a gasar tamaula ta Sifaniya.

Ya fara buga gasa mai daraja ta biyu a Sifaniya a 2008 daga nan ya samu gurbin shiga La Liga a 2017.

Kaka biyu Girona ta yi a La Liga daga nan ta yi shekara uku a rukuni na biyu daga baya ta koma buga La Liga a kakar da ta wuce.

Karawa tsakanin Barca da Girona

Kungiyoyin biyu sun kara a bana ranar 28 ga watan Janairu, inda Barcelona ta je ta ci 1-0, Pedri ne ya ci mata kwallon a minti na 61.

A wasa hudu baya da suka kara a lokacin da Girona ke buga La Liga, Barca ce ta yi nasara a uku, yayin da Girona ta buga 2-2 a Camp Nou.

Bayani kan tsare baya a bana a La Liga tsakanin kungiyoyin: