You are here: HomeAfricaBBC2022 12 13Article 1679891

BBC Hausa of Tuesday, 13 December 2022

    

Source: BBC

Abin da sabbin dokokin korona na matafiya da aka sauya a Najeriya ke nufi

Masu tafiya a filin jirgin sama Masu tafiya a filin jirgin sama

Gwamnatin Najeriya ta kawo karshen tilasta sanya takunkumi ga ma'aikata a tashar jiragen sama da kuma fasinjoji.

Mutanen da takunkumi ya kasancewa wajibi a yanzu su ne wadanda suka haura shekaru 60.

Matakin gwamnatin kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta ce daga yanzu matafiya sun daina nuna sakamakon gwajin cutar korona idan sun isa ko kuma za su yi tafiya zuwa wata kasa.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar ta ce an ɗauki matakin ne bayan tabbatar da cewa a yanzu ba kasafai ake samun wadanda suka kamu da cutar ba a Najeriya dama sauran kasashen duniya.

  Me ke kunshe cikin sabbin dokokin Koronar?

Kusan a yanzu gwamnatin Najeriya ta gamsu cewa ba a fiya samun wasu dauke da korona ba a kasar.

Kuma bincikenta ya tabbatar da cewa ko a wasu kasashen adadin masu kamuwa da cutar ya ragu matuka.

Don haka kwamitin da ke yaki da annobar korona da aka kafa ta janye ko sassauta dokokinta 19 da ya zama wajibi mafiya a cikin gida da kuma masu shigowa su mutunta.

Bulaguron cikin gida

"Ga masu tafiye-tafiyen cikin gida, sanya takunkumi a tashar jirgi ko a cikin jirgi ga ma'aikata da fasinjoji da matukan jirgi ba wajibi ba ne," in ji sanarwar.

Gwamnati ta ce ana baiwa duk wanda ya haura shekara 60 shawarar ci gaba da sanya takunkumi saboda kaucewa kamuwa daga cututtuka saboda raunin garkuwar jikinsu.

"Saboda dalilai irin su dashen wani sashe na jiki da sankarau da ciwon zuciya da ciwon suga da hawan jini, ana shawartar su cigaba da amfani da takunkumi, wanke hannunsu da ruwa da sabulu, amfani da man tsaftacce hannu da kuma kauracewa shiga taruka."

Wasu dokokin da za su daina aiki:

An daina yi wa kayan matafiya feshin magani kafin shiga tashar jirgin sama.

Daga yanzu za a dawo da bai wa matafiya abinci da lemuka da zarar sun shiga jirgi.

An daina bin dokar bai wa juna tazara a tashar jirgi ko wajen shiga jirgi.

Sai dai an shawarci a ci gaba da bin dokokin tsafta da shakar iska da yawan bin dokoki tabbatar da tsafta.

Akwai bukatar fasinjoji su yawaita tsaftace hannusu da man goge hannu.

An soke tsare-tsaren kai wa da komowa da aka bijiro da su saboda korona.

Bulaguron Ketare

Ba a bukatar gwajin korona ga fasinjoji da ke shirin fita ketare ko dawowa, ko da kuwa an yi maka rigakafi ko akasin haka.

An kuma dakatar da gwaji ga fasinjoji da suka karɓi cikakken riga-kafin.

Duk tsarin zai kasance guda tsakanin fasinjoji da ke tafiye-tafiye a cikin gida da kuma masu fita ketare ko dawowa.

Takardar sanin cikakkiyar lafiya

Ba a bukatar izinin neman tafiya ko tambarin da ake amfani da shi wajen samun bayanan matafiyi.

Yanzu wani fom na daban mai saukin cikewa za a dinga bai wa fasinjoji su cike, wanda ba shi da alaka da korona.

Fasinjoji za su cike wannan fom din kafin su fita ketare.

Fasinjojin da ba su samu damar cike fom din ba, to za a bukaci su yi hakan a cikin jirgi ko kuma idan sun isa tashar jirgi.

Sauran kasashen Afirka da suka sauya dokokin korona

Ba Najeriya ce kadai kasar Afirka da ta sassauta ko sauya dokokin yaki da annobar korona ba.

Kasashen Yammacin Afirka irinsu Ghana ma sun sassauta dokokin a ranar 1 ga watan Satumban 2022.

Ghana ta ce duk bakin da suka shiga kasarta, har daga kasashen yammacin Afika dole su tabbatar an yi musu cikakken riga-kafi.

Kuma dole su cike fom din da ke tabbatar da matakin lafiyarsu.

Ghana ta ce dole duk mutumin da ya haura 18 ya gabatar da fom da ke nuna ya karbi cikakken rigakafi.

Har yanzu kuma sanya takunkumi wajibi ne a Ghana.

A Kenya an soke duk wasu dokokin korona, bayan gwamnati ta dage duk haramcin da ta sanya a farkon wannan shekara.

An daina gwajin Korona ga fasinjojin da suka shiga kasar, sannan sanya takunkumi ba wajibi ba ne.

Ga Afirka ta Kudu, hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar, ta soke dokar da ta bukaci sai marasa cutar ko wadanda suka warke kadai ke iya tafiya zuwa Amurka.

Read full article