You are here: HomeAfricaBBC2021 12 27Article 1432198

BBC Hausa of Monday, 27 December 2021

    

Source: BBC

Afghanistan: Taliban ta hana mata tafiya ba muharrami

Daya acikin shuagabanin Taliban Daya acikin shuagabanin Taliban

Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce daga yanzu duk matan da za su yi wata doguwar tafiya, ba za a bari su hau mota ba sai suna da rakiyar muharraminsu (dan uwa namiji na kusa).

Ma'aikatar wanzar da da'a da yaki da aikata miyagun ayyuka wadda ta fitar da dokar, ta kuma umarci dukkanin masu ababen hawa daga yanzu kada su sake daukar duk wata mata sai wadda take sanye da hijabi.

Tun bayan da suka karbe iko da kasar ta Afghanistan a tsakiyar watan Agusta ‚yan Taliban din suke sanya dokoki a hankali a hankali na takaita wa mata walwala.

A wannan sabuwar dokar, Ma'aikatar wanzar da da'a da yaki da aikata miyagun ayyuka ta gwamnatin ta Taliban ta ce daga yanzu duk matar da za ta yi bulaguron da ya kai na nisan kilomita saba'in, dole ne ta samu rakiyar wani muharraminta.

Haka kuma dole ne duk matar da za ta yi tafiya ta sanya hijabi, inda gwamnatin ta umarci direbobi da kada su dauki duk matar da ba ta sanya hijabi ba.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta soki sabbin dokokin na gwamnatin Taliban, inda ta ce dokokin kusa suke da mayar da mata 'yan fursuna, ta hanyar hana musu damar zirga-zirga ba tare da wani tarnaki ba.

Fitacciyar mai rajin kare hakkin mata a Afghanistan din Wazhma Frogh, ta gaya wa BBC cewa ba ta yi mamaki ba da sabbin dokokin na Taliban.

Ta ce, '' ban ga wani jami'in diflomasiya na duniya ko na waje ba da ke magana da Taliban a kan mene ne sharuddansu ba.

Dukkanin wadannan tawagogin na waje da ke zuwa Kabul, ba sa ma ganawa da matanmu saboda suna tsoron Taliban.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suna kokarin gaya wa ma'aikatansu 'yan mata masu shekaru sama da goma su zauna a gida saboda kada su tunzura Taliban.

Duk abin da muka gani daga gwamnatocin Birtaniya da Turai da Amurka zuwa yanzu na nuna cewa kamar sun mika wuya ne ga bukatun."

Haka kuma gwamnatin ta Taliban ta haramta sanya kida a motoci.

Daman kuma tun a makonnin baya Taliban din ta umarci tashoshin talabijin da su daina sanya fina-finai da wasannin kwaikwayo da ke da mata a ciki.

Tun bayan faduwar gwamnatin kasar ta Afghanistan mai samun goyon bayan gwamnatocin yammacin duniya, makaratun sakandire na mata a yawancin larduna har yanzu suna rufe.

Kasashen da ke ba kasar tallafi sun gindaya wa Taliban din sharadin mutunta hakkin mata kafin su dawo da bayar da taimakon kudin da suke yi

Read full article