You are here: HomeAfricaBBC2022 06 08Article 1556417

BBC Hausa of Wednesday, 8 June 2022

    

Source: BBC

Afirka ta Kudu: An cafke iyalan Gupta a Hadaddiyar Daular Larabawa

Hoton Atul Gupta da Jacob Zuma tsohon shugaban Afrika ta kudu Hoton Atul Gupta da Jacob Zuma tsohon shugaban Afrika ta kudu

An cafke 'yan uwan juna, kuma hamshakan attajiran nan da suka janyo ce-ce-ku-ce a Afirka ta Kudu wato Rajesh Gupta da Atul Gupta a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wanna na zuwa ne, watanni hudu da 'yan sandan kasa da kasa na Interpol suka fara farautarsu, kan zargin cin hanci da rashawa. Ga fassarar rahoton wakilin BBC Vumani Mkhize

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta tabbatar da cafke iyalan na Gupta, kuma tuni suka shiga hannun hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ana zargin Rajesh da Atul Gupta halasta kudaden haram, da suka kai dala miliyan 1 da dubu 500, da hannu wajen juya akalar ayyukan da gwamnati ke yi ga kamfaninsu, a lokacin zamanin mulkin tsohon shugaban kasar Jacob Zuma saboda alakar da ke tsakaninsu, wanda shi ma yake fuskantar shari'ar cin hanci da rashawa, da almubazzaranci da dukiyar kasa, ko da ya ke ya sha musanta zargin.

An kuma fara batun taso keyarsu zuwa Africa ta Kudu domin fuskantar shari'a kamar yadda hukumomi suka bayyana.

'Yan uwan dai sun tsere daga Afirka ta Kudu ne , bayan hukumar shari'ar kasar ta fara bincike kan zargin hannunsu a wata danbarwar rashawa a shekarar 2018.

An tuhume su da ba da na goro, domin samun wata gagarumar kwangila daga gwamnati, da samawa mutane manyan mukaman gwamnati.

Manyan tuhume-tuhumen da ake yi wa fitattun 'yan kasuwar haihuwar Afirka ta Kudu asalin Indiya dai, ta fi karfi kan alakarsu da Mista Zuma tun lokacin da ya zama shugaban kasa a shekarar 2009, kafin a tilasta ma sa sauka daga mukami kan zargin almundahana shekaru tara da suka gabata.

Read full article