BBC Hausa of Thursday, 20 July 2023
Source: BBC
Liverpool ta amince da yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 12 tare da karin tsarabe-tsarabe don sayar da kyaftin din kungiyar Jordan Henderson ga kungiyar Al-Ettifaq ta Saudiyya.
Henderson ya je Jamus ne tare da Liverpool don yin atisaye, amma bai shiga wasan sada zumuncin da suka doke Karlsruher da ci 4-2 ba.
Dan wasan tsakiyar Ingila, mai shekara 33, yana da sauran shekaru biyu a kwantaraginsa a Anfield.
Kwanan nan ne aka nada tsohon kyaftin din Liverpool Steven Gerrard a matsayin kocin Al-Ettifaq.
Yarjejeniyar Henderson ta biyo bayan tayin fan miliyan 40 da Liverpool ta samu daga Al-Ittihad kan dan wasan tsakiyarta Fabinho a ranar Juma'ar da ta gabata.
Manyan ‘yan wasa da dama ne suka koma kasar Saudiyya a bana, wadanda suka hada da tsohon dan wasan Real Madrid, Karim Benzema da tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea N’Golo Kante.
Tsohon dan wasan Liverpool Roberto Firmino ya koma Al-Ahli bayan karewar kwantiraginsa a Anfield.
Henderson ya koma Liverpool ne daga Sunderland a kan fam miliyan 20 a watan Yunin 2011.
Henderson dai ya buga wa Reds wasanni 43 a kakar wasan da ta wuce, yayin da ta sha fama da rashin nasara, inda ta kare a mataki na biyar a teburin gasar Premier, kuma ba ta samu gurbi a gasar zakarun Turai ba.
Gaba ɗaya, ya buga wa Reds wasanni 492, inda ya zura kwallaye 33 a raga.
Henderson ya kasance kyaftin lokacin da Liverpool ta lashe gasar zakarun Turai a shekarar 2019 kafin ta ci kofin Uefa Super Cup da kuma Fifa Club World Cup daga baya a wannan shekarar.
Ya kuma kasance kyaftin na Reds lokacin da kulob din ta lashe gasar Premier ta 2019 zuwa 2020 don kawo karshen shekaru 30 na jiran kofin gasar Premier ta Ingila.
Sauran abubuwan karramawa da Henderson ya samu a Liverpool sun hada da lashe kofin FA a 2022 da League Cup a 2012 da 2022.