BBC Hausa of Thursday, 22 June 2023
Source: BBC
Samun ɗan lokaci don rintsawa akai-akai, yana da matuƙar alfanu ga lafiyar ƙwaƙwalwa kuma yana taimaka wa bunƙasar ƙwaƙwalwa tsawon lokaci, a cewar masu bincike daga Jami'ar University College London.
Rukunin masanan ya nuna cewa ƙwaƙwalwar masu taɓa ƙailula ko barcin rana tana kan ma'aunin kyubik sentimita 15, daidai da matakin da za ta iya rage tsufa da kusan shekara uku zuwa shida.
Sai dai kuma, masana kimiyyar sun bayar da shawarar cewar barcin, kada ya kai na rabin sa'a.
A cewar ƙwararrun, barcin rana yana matuƙar wahala ga ma'aikata a fannonin sana'o'i da dama, inda a wasu wuraren aikin ake ganin baiken masu taɓa ƙailula.
"Muna ba da shawara cewa kowa ne mutum zai iya samun amfani daga barcin," kamar yadda Dakta Victoria Garfield ta faɗa.
Ta bayyana sakamakon da aka gano da cewa "sabo ne fil kuma mai matuƙar ƙayatarwa".
Barcin rana, muhimmin abu ne ga bunƙasar rayuwar ɗan'Adam a lokacin da muke jarirai, sai dai muna girma, yana daɗa raguwa amma yakan sake ƙaruwa a lokacin da muka yi ritaya daga aiki, an ba da rahoton cewa kashi 27 cikin ɗari na mutanen da suka haura shekara 65 suna gyangyaɗawa da rana.
Dakta Garfield ta ce shawarar yin barcin rana "aba ce mai matuƙar sauƙi" idan aka kwatanta da rage kiba ko kuma motsa jika wadanda ke da "wahala a wajen galibin mutane".
Kaifin ƙwaƙwalwa bisa tsarin rayuwa yana disashewa yayin da shekaru ke ƙaruwa, amma shin ko barci yana taimakawa wajen yin kandagarkin cutuka kamar susucewar tunani, wannan wani abu ne da har yanzu yake buƙatar ƙarin bincike.
Lafiyar kwakwalwa tana da matuƙar muhimmanci wajen ba da kariya ga cutar tsananin mantuwa kuma larurar tana da alaka da katsewar barci.
Masana sun ba da shawarar cewa rashin isasshen barci yana lalata ƙwaƙwalwa a tsawon lokaci, kuma yana haddasa zogi sannan yana shafar jijiyoyin sadarwa tsakanin ƙwayoyin halittar jiki.
"Don haka, gyangyaɗi lokaci-lokaci yana iya kare mutum daga larurar mantuwa ko daina aikin ƙwayoyin halittun jijiyoyin laka ta hanyar rama tauyewar barcin da aka samu da dare," a cewar jami'ar bincike Valentina Paz.
Sai dai Dakta Garfield na da ra'ayin cewa maimakon ta samu wuri mai taushi ta kwanta ta yi ƙailula gwamma ta motsa jiki tsawon minti 30, amma ta ce za ta iya bai wa mahaifiyarta shawarar ta yi irin wannan barcin.
Ta yaya za a samu amsa?
Yin nazari a kan barci zai iya zama ƙalubale.
Barci zai iya ƙara lafiya, sai dai hakan yana iya tabbata ne idan jiki ya gaji kuma yana buƙatar barci.
Masana sun yi amfani da dabaru iri daban-daban wajen gano amfanin da barci ke da shi.
Sun yi amfani da gagarumar hanyar gwajin gudan halitta na DNA a jikin ɗan'Adam.
Binciken da aka gudanar a baya ya gano gudan halittar DNA na mutum 97 da ke iya sanya barci ko kuma kasa yin barcin da rana.
Rukunin masu binciken ya ɗauki samfur daga jkin mutum 35,000, 'yan shekara 40 zuwa 69, wadanda aka sanya wajen adana kwayoyin halitta na kasar Birtaniya, kuma sun kwatanta kwayoyin halittar masu yin barci da wadanda ba sa yi.
Sakamakon da aka wallafa a mujallar lafiya ta Sleep Health, ya nuna bambanci a tsakanin kyubik sentimita 15.
Adadin jimillar kwakwalwar ya kai kyubik sentimita 1,480, kamar yadda binciken ya nuna.
"Ina jin dadin dan gajeren barci a karshen mako kuma wannan binciken ya kara gamsar da ni cewa bai kamata na zama mai kasala saboda barci ba, har ma yana iya baiwa kwakwalwata kariya," inji Farfesa Tara Spires-Jones, daga jami'ar Edinburgh, kuma shgaban kungiyar masana kimiyyar lafiyar kwakwalta ta kasar Birtaniya.
Masana ba su yi nazari kai tsaye game da yin barci mai nauyi a tsakiyar rana ba, sai dai sun ce binciken ya yi nuni da cewa yana tasiri ne a kasa da rabin sa'a.