BBC Hausa of Friday, 23 June 2023
Source: BBC
An yanke hukuncin daurin shekaru 9 ga wata mata Bajamushiya mabiyar kungiyar masu da'awar kafa daular Musulunci ta IS bisa zarginta da laifukan da suka hada da bautar da wata mata mai bin addinin Yazidi.
Ana kuma tuhumar matar da laifin cin zarafin ɗan'Adam sannan da zama mamba a kungiyar 'yan ta'adda ta duniya.
Wata kotu a yammacin birnin Koblenz ta ce matar 'yar shekara 37 ta ci zarafin matashiyar mai bin addinin Yazidi har tsawon shekaru uku a lokacin da suke rayuwa a Syria da Iraqi.
An kuma same ta da laifin karfafa wa mijinta gwiwa don yin lalata da lakada wa matar duka.
"Dukkan wadannan al'amurra manufofi ne na kungiyar IS, domin kawar da akidar addinin Yazidi," a cewar masu gabatar da kara a lokacin da aka fara shara'ar a watan Janairu.
A shekarar 2014, mayakan IS sun afka wa garin da aka fari addinin Yazidi da ke yankin Sinjar a arewacin Iraqi inda suka kaddamar da abin da majalisar dinkin duniya ta kira da yunkurin kisan kare-dangi.
Dubban mutane da suka hada har da kananan yara 'yan shekaru 12 aka hallaka bayan cikar wa'adin da aka ba su na neman su sauya addininsu ko kuma a kashesu.
Mata da 'yan mata 7,000 ne aka mayar da su bayi da kuma cin zarafinsu.
Daga cikin mutanen da masu gabatar da karar suka zarga an ci zarafinsu akwai wata matashiya mai suna Nadine K, da mijinta wadanda aka mayar da su bayi daga shekarar 2016, a lokacin da suka koma birnin Mosul da ke arewacin Iraqi.
Sun tafi zuwa Syria da zummar shiga kungiyar IS bayan shekara guda, daga bisani suka koma tare da matar, wacce take da shekaru 20 a wancan lokacin.
A watan Maris na 2019, mayakan Kurdawa na Syria suka kama Nadine K da iyalant.
An kama ta a bara bayan tisa keyarta zuwa Jamus.
A lokacin da ake shara'ar, matar da ake tuhumar ta musanta zargin da ake mata na tilasta wa mabiyar addinin Yazidi amma ta ce ta yi mata abubuwa da dama.
Matar, wadda aka kubutar a 2019, an tabbatar a shara'ar da aka yiwa Nadine K, a watan Fabarairu kuma ta halarci zaman hukuncin da aka yanke a ranar Laraba.
Lauyanta ya ce dukkan wadanda ake karar suna fatan dukkan wadanda aka samu da laifi makamancin wannan a zartar musu da hukunci, kamar yadda kamfanin dillanci na Associated Press ya bayyana.
A baya bayan nan akwai shara'oi da dama da ake gudanarwa a Jamus da suka shafi tsoffin magoya bayan kungiyar IS inda ake zarginsu da kashewa ko kuma cin zarafin mabiya addinin Yazidi.
A watan Oktoban 2021, an yanke hukuncin daurin shekaru 10 ga wata mata sakamakon kisa wata matashiya mai bin addinin Yazidi wadda ita da mijinta aka saya a matsayin bayi.
Wata guda gabanin hakan, wata kotu a Jamus ta gudanar da shara'a irinta ta farko a duniya wacce ta zartar da hukuncin dake nuna cewa laifukan da 'yan IS suka aikata kan mabiya addinin Yazidi kisan kare-dangi ne.