BBC Hausa of Friday, 9 June 2023
Source: BBC
Kimanin marayu 300 ne da musayar wuta ta rutsa da su a Khartoum, babban birnin Sudan jami'an bayar da agaji suka ceto a wani yanayi mai cike da hatsari.
An dai kwashe yaran ne bayan mutuwar jarirai 67 a gidan marayu na Mygoma da ke birnin Khartoum.
Sun mutu ne sakamakon yunwa da rashin ruwa da kuma cututtuka yayin da faɗa ya hana ma’aikatan isa gidan marayu.
Khartoum dai na fuskantar hare-hare ta sama a kullum da kuma kazamin faɗa tsakanin dakarun da ke gaba da juna tun ranar 15 ga Afrilu.
Gidan marayun dai na wani yanki ne da ke zaman cibiyar faɗa tsakanin sojoji da dakarun sa-kai na Rapid Support Forces (RSF).
A wani samame mai hatsarin gaske, yara 297 - kimanin 200 daga cikinsu 'yan kasa da shekaru biyu - an kai su ta hanyar mota zuwa wani wuri da ke da zaman lafiya a Wad Madani da ke kudancin Sudan.
A cikin ƙarshen mako wasu masu fafutuka sun kwashe kimanin yara 95 daga gidan marayu na Mygoma da sauran ƙananan wurare a babban birnin kasar.
Akwai yara kimanin 400 a gidan marayun na Mygoma wanda ke ƙarƙashin kulawar gwamnati, lokacin da yaƙin ya barke a watan Afrilu.
Ƙoƙarin da likitoci suka yi na isa gidan marayun domin ceto su ya zamo abu mai haɗari.
Rashin samun isasshen ƙarfin lantarki da raguwar ruwan famfo da ake samarwa sun sanya yanayin zafi ya kai maki 43c a ma'aunin salshiyas, lamarin da mutane ba za su iya jurewa ba.
Hakan ya sanya yara ƙanana suka fara mutuwa.
"Muna rasa su cikin sauri. A cikin 'yan kwanakin nan, mun rasa 'ya'ya uku," in ji wata ƴar gwagwarmaya a ƙasar ta Sudan, Sadeia al-Rasheed Ali Hamid a tattaunawarta da BBC.
Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya, Unicef, ta ce marayu 67 ne suka mutu a gidan marayun na Mygoma daga ranar 15 ga Afrilu.
Masu fafutuka na cikin gida da kungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa sun yi kokarin fitar da yaran daga yankin, amma hakan bai zo da sauki ba.
Tattaunawar tsagaita bude wuta a birnin Jeddah na kasar Saudiyya ta ruguje kuma an sake ci gaba da gwabza fada.
Akwai alubalen sufuri wajen ɗauke ɗaruruwan yara da jarirai zuwa wurin da babu tashin hankali.
Sai dai Sadeia ta ce babu zaɓi.
Tare da haɗin gwiwar wasu ƴan ƙasar ta Sudan, ta shirya kwashe yara masu shekaru tsakanin huɗu zuwa 15 a sirrance.
“Mun ciro su daga wuraren da tabbas za su iya mutuwa zuwa wani wuri da nake fata ya fi aminci da mutunci,” in ji Heba Abdullah, wata mai kula da gidan marayun da ta yi tafiya tare da su.
Wannan ayarin motocin bas na farko sun tashi a lokacin fadan, inda suka wuce shingayen bincike da dama.
An yi wa kungiyar maraba a wata makaranta a garin al-Hasaheisa da ke kudancin Khartoum.
Amma bayan matsuguni da abinci da mazauna wurin ke bayarwa, babu wani taimako da ke jiran yaran.
Heba ta ce "Ba da jimawa ba, daya daga cikin makwabta ta tambaye ni abin da muke bukata, ta ce ba ta da wani abu da za ta iya bayarwa, amma za ta taimaka,"
Aikin da ya fi wahala shi ne fitar da ƙananan yara.
Masu taimako na cikin gida da kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) da Unicef sun yi aiki tare da ma'aikatar lafiya ta Sudan don shirya ayarin motocin bas daga Khartoum.
Tafiyar sa'o'i hudu ce muka yi, inda muke jin ƙarar yadda ake artabu daga nesa.
Kimanin yara miliyan 13 aka kiyasta rikicin ya rutsa da su, kuma yayin da ake ci gaba da gwabza fada, fatan samun sulhu cikin gaggawa na dushewa.
Kwashe marayun, in ji Ms Eagleton, shi ne babban abin da ake fata.
"Ya kawo haske ga dukanmu."