BBC Hausa of Sunday, 19 February 2023
Source: BBC
An fitar da Neymar daga fili a kan gadon marasa lafiya a wasan da Paris St Germain ta doke Lille 4-3 a gasar Ligue 1 ranar Lahadi.
Kylian Mbappe da Neymar suka fara ci wa PSG kwallaye daga baya Lille ta zura uku ta hannun Bafode Diakite da Jonathan David da kuma Jonathan Bamba.
Daga baya Mbappe ya kara na biyu, sannan Lionel Messi ya zura na hudu a ragar Lille a bugun tazara.
Neymar ya ji rauni a karawar a mintuna kadan da komawa zagaye na biyu, inda likitocin aikin gaggawa suka fitar da shi daga filin.
Ya nuna yana shan radadi, wanda ya rufe fuskarsa da hannayensa a lokacin da ake kokarin fitar da shi a kan gadon marasa lafiya a Parc des Prince.
PSG ta kawo karshen wasa uku a jere da aka doke ta.
Da wannan sakamakon PSG ta bayar da tazarar maki takwas a teburin Ligue 1 kafin wasan Marseille ta biyu a teburi da za ta fafata da Toulouse ranar Lahadi.
Tun farko PSG ta sauya mai tsaron baya, Nuno Mendes, wanda ya ji rauni a karawar, sannan Neymar.
PSG za ta buga wasa na gaba a Ligue 1 ranar 26 ga watan Fabrairu, inda za ta ziyarci Marseille.