You are here: HomeAfricaBBC2023 04 25Article 1755452

BBC Hausa of Tuesday, 25 April 2023

    

Source: BBC

An kashe kuɗin da ba a taɓa ɓatarwa ba a yaƙi a duniya a 2022 - Rahoto

Hoton alama Hoton alama

Wata cibiyar gudanar da bincike a kan rikice-rikice a duniya wadda ke Sweden ta ce mamayen da Rasha ta yi wa Ukraine da kuma zaman tankiya da ake yi a gabashin Asia sun taimaka wajen gagarumar karuwar kudaden da ake kashewa a aikin soji zuwa matakin da ba a taba kaiwa ba a duniya.

Cibiyar ta Stockholm International Peace Research Institute ( SIPRI), ta ce kudaden da ake kashewa yanzu sun kai dala tiriliyan 2.24 a shekarar da ta wuce, 2022.

Hakan na nufin an samu karuwa da kashi 3.7 cikin dari saboda tashin farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.

Alkaluman cibiyar sun hada da kudaden da ake kashewa a kan makamai da na kula da dakaru da gudanarwa da bincike da kuma bunkasa ayyukan na soji.

Cibiyar ta ce alkaluman da ta fitar sun nuna wannan karuwa da aka samu ta kudaden da ake kashewa a kan sojin, tsaro na kara raguwa ne a duniya.

Kuma kamar yadda ba za a yi mamaki ba, yakin da ake yi a Ukraine shi ne kang aba wajen haddasa gagarumar karuwar kasha kudaden.

A fadin Turai da wasu sassan duniyar.

Cibiyar ta yi kiyasin cewa kudaden da Rasha ke kashewa a harkar soji abin da kasar ba ta bayyanawa, sun karu da sama da kashi tara cikin dari

Rashar ita ce ta uku a tsakanin manyan masu kasha kudi a harkar soji a duniya, amma kuma duk da haka ba ta ma kasha daya bisa uku na abin da China ke batarwa.

Sannan ita ma Chinar kuma binciken ya nuna kasafinta a harkar tsaron kasha daya ne bisa uku kawai na abin da Amurka ke kashewa

Ita kuwa Ukraine kudin da take kashewa a tsaro ba a hada da taimakon da ake ba ta daga kasashen duniya, ya yi tashin gwauron zabi da sama da kashi 640 cikin dari.

Kuma wannan shi ne karin da cibiyar ta taba samu wanda ya fi girma a cikin shekara daya kacal a tarihin bincikenta na sama da shekara saba’in.

Kuma rikicin na Ukraine ya sa an samu karuwar kudin da ake kashewa a tsaro a tsakanin kasashen tsakiya da kuma yammacin Turai zuwa wanda ba a taba gani ba tun bayan yakin cacar baka.

Bayan Rasha Birtaniya it ace ta fi kasha kudi a harkar ta soji a Turai, kuma ita ce ta shida a duniya.

Kudaden da take kashewar a yanzu sun karu da kashi 3.7 cikin dari, kusan saboda kasancewarta ta biyu cikin wadanda suka fi tallafa wa Ukraine bayan lamba daya, Amurka.

Cibiyar binciken ta kuma nuna yadda ake samun karuwar kudaden da ake kashewa a harkar tsaro a yankin Asia.

Nazarin ya nuna cewa abin da China take kashewa ya karu da sama da kashi hudu cikin dari kasancewar kasafin nata na karuwa a duk shekara tsawon kusa da shekara talatin.

Duk da cewa rahoton bai fayyace dalilin samun hakan ba, amma ana ganin ba zai rasa nasaba da batun Taiwan ba, inda ake ta samun karuwar zaman zullumi a kullum a kan batun tsibirin wanda China ke daukansa a matsayin wani bangare nata.

Ita ma Japan kudin da take kashewa a ayyukan sojin ya karu da kusan kashi shida cikin dari, duk da dai cewa ta fara ne sannu a hankali in ji rahoton.

A bara ne Japan din ta sanar cewa za ta rubanya abin da take kashewa a harkar soji a cikin shekara biyar, tana mai danganta hakan da barazanar da China da Koriya ta Arewa da kuma Rasha suke yi mata.

Ita ma India ba a bar ta a baya ba, domin kasafin nata ya karu da kashi shida cikin dari, yayin da take rikicin kan iyaka da Pakistan da kuma China.

A yankin Gabas ta Tsakiya kuwa Saudi Arabia ta kashe madudan kudade a kan soji, inda a bara ta kasha dala miliyan dubu 75 a kiyasin cibiyar mai wannan nazari,inda babban abin da ya kai ta wannan shi ne shiga rikicin Yemen.

Wannan kiyasi ya sa Saudiyyar ta kasance ta biyar da ta fi kashe kudi a fannin tsaro a duniya, inda take bayan India.

Sai dai kuma wannan rahoto ya nuna raguwar kasha kudaden a ayyukan tsaron a fadin Latin Amurka da kuma kasashen Amurka ta Tsakiya da yankin Karebiyan.

Ita kuwa Afirka nahiyar Afirka in banda Habasha wadda ta samu kanta a bangaren wadanda ke kasha karin kudaden sakamakon rikicinta na Tigray, kusan naihyar gaba daya ta samu raguwar kudaden da take kashewa na sojin.

A Najeriya abin da hukuma ke kashewa ya ragu da sama da kashi daya bisa uku

duk da matsalar tsaro da kasar take fama da ita ta masu ikirarin jihadi, in ji rahoton na cibiyar nazarin harkokin tsaron da ke Sweden.

Rahoton ya ce mummunar barnar da ambaliyar ruwa ta haifar a kasar a bara kusan ita ce ta sa gwamnati ta rage abin da take kashewa a tsaron ta karkata kan wannan barna ta ruwa.

Read full article