You are here: HomeAfricaBBC2023 04 28Article 1757192

BBC Hausa of Friday, 28 April 2023

    

Source: BBC

An sa sunan Pelé gwarzon ɗan ƙwallon duniya a ƙamus ma'anarsa 'na-daban'

Marigayi Pele Marigayi Pele

Laƙabin Pelé, da ake faɗa wa marigayi gwarzon ɗan ƙwallon duniya, bisa ƙa'ida ya shiga cikin ƙamus, inda yake nufin "zaƙaƙuri ko fintinkau ko abu na daban".

Ƙamusun harshen Fotugal (Portuguese) mai suna Michaelis, ɗaya daga cikin mafi shahara a Brazil, ya sa sunan "pelé" a matsayin sabuwar kalmar siffa a kundinsa na intanet.

Sanya sunan a cikin ƙamusu, ya zo ne bayan wani gangami da Gidauniyar Pele ta ƙaddamar na neman a karrama tauraron ɗan ƙwallon, inda ya samu amincewa har mutane fiye da 125,000 suka sa hannu.

Pele dai ya mutu a watan Disamban bara yana da shekara 82.

Shi kaɗai ne ɗan ƙwallon da ya ci Kofin Duniya sau uku, kuma mutane da yawa na ɗaukar sa a matsayin ɗan ƙwallon ƙafa mafi fice a tarihi.

A lokacin sana'arsa ta ƙwallon ƙafa tsawon shekara 20, ya ci ƙwallayen masu yawa a tarihi har 1,281 lokacin da ya buga wa ƙungiyar Santos ta Brazil da kuma a ƙasar Brazil da kulob ɗin Cosmos na New York.

Read full article