You are here: HomeAfricaBBC2021 08 16Article 1334305

BBC Hausa of Monday, 16 August 2021

    

Source: BBC

An sace ɗalibai da malamai a Kwalejin Noma ta Bakura a Jihar Zamfara

Rashin tsaro ya jefa mutane da dama a cikin 'tsaka mai wuya' Rashin tsaro ya jefa mutane da dama a cikin 'tsaka mai wuya'

Rahotanni daga jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya na cewa an sace ɗalibai da malamai a Kwalejin Noma da ke garin Bakura.

Mataimakin rijistara na kwalejin Malam Aliyu Bakura, ya tabbatar wa da BBC wannan labari.

Ya ce "a jiya Lahadi da daddare wajen ƙarfe 10 suka shiga suka yi ta harbe-harbe suka kwashe ɗalibai 15 da kuma wani malami da matarsa da ƴaƴansa biyu," a cewarsa.

Read full article