You are here: HomeAfricaBBC2023 01 03Article 1689878

BBC Hausa of Tuesday, 3 January 2023

    

Source: BBC

An saka wa jarirai 738 sunan Pele a Peru

Pele Pele

Yayin da ake ci gaba da jana'izar shahararren dan kwallon Brazil da ma duniya baki daya wato Pele, hukumar da ke yi wa jarirai rajista a Peru ta ce iyaye 738 ne suka saka wa ya'yan da suka haifa sunan mamacin.

Kamar yadda rajistar da ke dauke da sunayen ta nuna, an rika saka sunayen daban daban kamar Pele, King Pele, Edson Arantes, ko kuma Edson Arantes do Nascimento, wanda shi ne cikakken sunan na Pele.

Pele ya mutu ranar Alhamis, bayan fama da cutar kansa yana da shekaru 82.

Yanzu haka al'umma na ci gaba da jerin gwano a birnin Santos, don yin tozali da gawar ta Pele.

A Santos ne Pele ya fara wasa tun yana matashi, kuma mafi yawan kwallayen da ya ci sama da 1000 a nan ne ya ci su.

Daga cikin masu ta'aziyar Pele akwai sabon Shugaban Brazil Lula da Silva, da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino da ma wasu yan wasan Brazil.

Read full article