BBC Hausa of Thursday, 9 February 2023
Source: BBC
Hukumar kwallon kafar Ingila ta tuhumi Manchester United da Crystal Palace da tada jijiyar wuya a Old Trafford ranar Asabar a Premier League.
Lamarin ya faru, bayan jan katin da aka yi wa dan wasan United, Casemiro, sakamkon shakar wuyan Will Hughes da ya yi.
An tuhumi kungiyoyin biyu da kasa tsawatarwa 'yan wasansu a karawar ta babbar gasar tamaula ta Ingila.
FA ta ce ''United ta kasa hana 'yan wasanta yin halayyar da za ta iya tayar da yamutsi'' a karawar.
Hatsaniyar ta barke a minti na 67 a wasan da United ta yi nasara 2-1, bayan da dan kwallon Palace, Jeffrey Schlupp ya hankade Antony zuwa allon tallace-tallace na gefen fili.
Ten Hag ya bukaci VAR ttake sa ido sosai, bayan da aka bai wa Casemiro jan katin.
Dukkansu 'yan wasan an ba su katin gargadi mai ruwan dorawa daga baya mai kula da VAR, Tony Harrington ya ga hannun Casemiro a wuyan dan wasan Palace, Hughes.
Dan kasar Brazil na hukuncin dakatarwa wasa uku kenan, bai yi wa United karawar da ta tashi 2-2 da Leeds United ranar Laraba ba.
An bai wa kungiyoyin nan da ranar Litinin 13 ga watan Fabrairu domin su wanke kansu, ko a dauki matakin doka.