Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya, ya ce babu wani dalilin da zai sa ya yi nadama kan yadda ya gudanar da aikinsa ko da kuwa matakan da ya ɗauka ba su yi wasu mutane daɗi ba.
A wata hirar da ya yi da BBC Hausa, Janar Monguno ya ce babban ƙalubalen da ya fuskanta shi ne taƙaddamar da ya rinƙa yi da mutane da kuma kungiyoyi kan matakan da ya ɗauka musamman kan hana shigowa da miyagun abubuwa Najeriya.
"Da na zo sai na ce babu wanda zai laɓe karkashin ma'aikatana su sami waɗannan abubuwan, wannan abin ya tayar wa mutane da yawa hankali amma ba abin da zai sa in yi nadama ba ne. An yaƙe ni ƙwarai da gaske." A cewarsa.
Janar Monguno, ya ce cikin shekaru biyu da suka wuce, ofishinsa ya yi iyakacin ƙoƙarinsa wurin yaƙi da yaɗuwar ƙananan makamai a inda ya buƙaci haɗin kan al'umma wurin samun bayanai da za su taimaka wajen hana shigowa da makaman.
Ba mu da masaniya kan ayyukan dakarun Birtaniya a Najeriya
Babagana Munguna ya kuma yi bayani kan batun da ake yi na cewa dakarun wasu ƙasashen ƙetare sun gudanar da wasu abubuwa a Najeriya.
Ya ce ba shi da wata masaniya kan labarin da ke cewa sojojin Birtaniya na musamman sun kai kusan shekaru goma suna aiki a asirce a cikin Najeriya.
A ranar Talatar da ta wuce wata jaridar Birtaniya ta fitar da wani rahoto cewa dakaru na musamman da aka fi sani da SAS na aiki a asirce a kasashe 19 ciki har da Najeriya tun shekara ta 2011.
Janar Munguno ya bayar da tabbacin cewa rahoto mai kama da wannan bai iso gare shi ba "Ni ban da wannan labarin domin bai zo ofishina ba, ƙila waɗansu jami'an sun samu amma babu wanda ya kawo min" a cewar sa.
Cikin shekara takwas da ya yi tare da shugaba Buhari, ya bayyana cewa ya bai wa shugaban ƙasar shawarwari da dama waɗanda suka yi tasiri wurin inganta mu'amullar Najeriya da sauran ƙasashe, tare da kawo cigaba a yaƙin da ake yi da matsalar rashin tsaro a cikin gida.