You are here: HomeAfricaBBC2022 10 02Article 1634603

BBC Hausa of Sunday, 2 October 2022

    

Source: BBC

Arsenal da Barcelona na zawarcin Neves, Man City za ta ƙara wa Haaland albashi

Ruben Neves Ruben Neves

Akwai rashin tabass game da makomar kocin Wolves Bruno Lage bayan rashin nasarar da suka riƙa samu tun farkon wasannin Firimiya da kuma yadda West Ham ta ci gaba da samun galaba a kan su. (Telegraph - subscription required)

Arsenal na fatan za ta riga Liverpool da Manchester United ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Wolves Ruben Neves mai shekara 25. (Express)

Ita ma  Barcelona za ta yi hamayya da Arsenal don sayan Neves. (Sport)

West Ham za ta fafata da AC Milan wajen sayan ɗan wasan gefen kulob ɗin Bruges Noa Lang mai shekara 23  (Calciomercato)

Manchester City za ta ƙara albashin ɗan wasan gabanta Erling Haaland mai shekara 22 sakamakon ƙwazon da ya nuna a farkon kakar wasa ta bana. (Star)

A cikin wani sabon shiri mahaifin Haaland Alf Inge ya ce a cikin shekaru uku zuwa huɗu ya ga ɗansa na wasa a City (Star)

Kawo yanzu ɗan wasan tsakiyar Barcelona Frenkie De Jong  mai shekara 25 na cikin sunayen ƴan wasan da ta ke son a yi musayar su. (ESPN)

Liverpool da Arsenal na rige -rigen ɗaukar dan wasan Norway Andreas Schjelderup wanda ya ke taka leda a kulob ɗin Nordsjaelland  kuma ana yi wa ɗan wasan laƙabi da Erling Haaland na gaba.  (Mail)

Arsenal na tunanin zawarcin ɗan wasan Bayern Leverkusen da Ecaudor Piero Hicapie mai shekara 20. (Teamtalk)

Jordan Henderson da  Trent Alexander-Arnold sun yi kira ga ɗan wasan tsakiyar  Borussia Dortmund  kuma ɗan wasan Ingila Jude Bellingham a kan ya koma taka leda da Liverpool. (Football Insider)

Sai dai ita ma Manchester United na shirin sake zawarcin ɗan wasan mai shekara 19 . (Express)

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce baya tunanin makormarsa a kulob ɗin duk da cewa kwantiraginsa zai zo ƙarshe a ƙarshen kakar wasa. (Manchester Evening News)

Read full article