You are here: HomeAfricaBBC2023 09 04Article 1837745

BBC Hausa of Monday, 4 September 2023

    

Source: BBC

Arsenal ta caskara Man United a mintunan ƙarshe a Premier

Yan wasan Arsenal Yan wasan Arsenal

Arsenal ta ci Manchester United 3-1 a wasan mako na huɗu a Premier League da suka kara a Emirates ranar Lahadi.

A minti na 27 da take leda Marcus Rashford ya fara ci wa United kwallo ya zama na biyu a United da ya ci Arsenal a wasa uku a jere, bayan bajintar Robin van Persie tsakanin 2012 zuwa 2013.

Minti ɗaya tsakani Martin Odegaard ya farke kuma daf da za a tashi Declan Rice ya ƙara na biyu, sannan Gabriel Jesus ya ci na uku.

Da wannan sakamakon Arsenal mai maki 10 ta ci wasa uku da canjaras daya shine wanda ta yi 2-2 da Fulham.

Man United mai maki shida ta ci wasa biyu an doke ta fafatawa biyu da fara kakar bana.

Ranar 17 ga watan Satumba Arsenal za ta ziyarci Everton, yayin da United za ta karbi bakuncin Brighton ranar 16 ga watan na Satumba.

Arsenal ta yi sauyin 'yan wasan a karawa da United, bayan tashi 2-2 da Fulham - yayin da Thomas Partey ke jinya bai buga fafatawar ba.

Gabriel da Oleksandr Zinchenko da Eddie Nketiah suka maye gurbin Jakub Kiwior da Partey da kuma Leandro Trossard.

Takehiro Tomiyasu ya fara daga zaman benci,bayan jinya da ya yi.

'Yan wasan Arsenal 11 da aka fara wasan da su:

Ramsdale, Gabriel, White, Saliba, Zinchenko, Odegaard, Rice, Havertz, Saka, Nketiah da kuma Martinelli.

Masu jiran ko-ta-kwana:

Tomiyasu, Jesus, Smith Rowe, Kiwior, Jorginho, Vieira, Raya, Nelson da kuma Trossard.

Canji daya Manchester United ta yi daga wadanda suka doke Nottingham Forest 3-2 - Victor Lindelof ya maye gurbin Raphael Varane.

Sabon dan wasan da United da ta dauka a bana Rasmus Hojlund ya fara da zaman benci tare da Altay Bayindir da Sergio Reguilon da kuma Jonny Evans.

'Yan wasan Manchester United 11 da aka fara wasan da su:

Onana, Wan-Bissaka, Lindelof, Martinez, Dalot, Casemiro, Eriksen, Antony, Bruno Fernandes, Rashford da kuma Martial.

Mau jiran ko-ta-kwana:

Bayindir, Maguire, Hojlund, Reguilon, Garnacho, Pellistri, Evans, Gore da kuma Hannibal.

Read full article