You are here: HomeAfricaBBC2021 09 28Article 1367227

BBC Hausa of Tuesday, 28 September 2021

    

Source: BBC

Arsenal ta ragargaji Tottenham a wasan hamayya

Bukayo Saka, dan wasan Ingila ya ci kwallo daya a gasar Bukayo Saka, dan wasan Ingila ya ci kwallo daya a gasar

Kungiyar Arsenal ta yi nasarar doke Tottenham da ci 3-1 a wasan Premier League da suka kara ranar Lahadi a Emirates.

Arsenal ta fara cin kwallo ta hannun Emile Smith-Rowe minti 12 da fara wasan, kuma matashin dan wasa da ya ci kwallo a wasan hamayya na birnin Landan mai shekara 21 da kwana 60 ranar Lahadi, tun bajintar da Alex Oxlade-Chamberlain ya yi a Satumbar 2014 mai shekara 21 da kwana 43.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya ci na biyu, sannan Bukayo Saka ya kara na uku a minti 34 da tsaka da karawar.

Shima Bukayo Saka ya zama matashin da ya ci kwallo, sannan ya bayar aka zura a raga a wasan na hamayya na birnin Landan mai shekara 20 da kwana 21 a ranar Lahadi, tun bayan kwazon da Cesc Fabregas ya yi a Satumbar 2007.

Sauran minti 11 a tashi daga karawar Tottenham ta zare kwallo ta hannun Heung-min Son.

Read full article