BBC Hausa of Tuesday, 2 May 2023
Source: BBC
Kociyan Arsenal Mikel Arteta yana son tattaunawa da dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, dan Ingila da zaran an kammala wannan kakar. (Mirror)
Haka kuma Gunners din na nazari kan sayen dan bayan Crystal Palace Marc Guehi, shi ma dan Ingila mai shekara 22. (Mail)
Chelsea na dab da nada tsohon kociyan Tottenham da Paris St-Germain Mauricio Pochettino a matsayin mai horad da kungiyar na dindindin. (90min)
Tayin da attajiri Sir Jim Ratcliffe ya yi na sayen mafi yawan hannun jarin Manchester United ya hada da cewa a ba shi iko a kan saye da sayar da 'yan wasan da kungiyar za ta yi ba tare da wani bata lokaci ba, idan cinikin ya fada. (Telegraph)
Manchester United ta tura masu nemo mata 'yan wasa su kalli wasan Tammy Abraham na Roma a karshen makon da ya wuce, saboda kungiyar na dubu yuwawar sayensa idan ta rasa Harry Kane na Tottenham. (Mirror)
Amma kuma Aston Villa tana da kwarin gwiwa cewa za ta saye Abraham din duk da sha'awarsa da manyan kungiyoyin Turai da dama ke yi. (90min)
Leeds United na nazari kan nada tsohon kociyan West Ham da Everton Sam Allardyce, wanda saura wasa daya ya rage masa a aikin horad da tawagar Ingila, domin ya maye gurbin Javi Gracia a matsayin kociyan kungiyar. (Athletic )
Aston Villa ta fara tattaunawa da dan gaban Ingila Ollie Watkins a kan tsawaita kwantiraginsa da kungiyar. (Athletic )
Wakilin Ansu Fati ya tabbatar wa da Barcelona cewa wata kungiya musamman ma daga Premier za ta sayi matashin dan Sifaniyar yuro miliyan 70 a bazara. (Sport )
Manchester United ta tashi haikan domin ganin ta yi nasarar sayen dan gaban Eintracht Frankfurt Kolo Muani na Faransa, a gogayyar da take yi da Bayern Munich kan dan gaban. (Sky Germany )
Wasu rahotanni na nuna cewa kociyan Feyenoord Arne Slot da Julian Nagelsmann, na gaba-gaba wajen samun aikin horad da Tottenham. (ESPN)
Haka kuma Tottenham din da Newcastle United na daga cikin kungiyoyin da suke jira su ga farashin da Southampton za ta sanya a kan dan wasan tsakiya na Ingila James Ward-Prowse, idan ta fadi daga Premier. (Mail)
Manchester City ba za ta hana Bernardo Silva, barin kungiyarsa ba idan har yana son tafiya a bazara. (90min)
Kociyan Crystal Palace Roy Hodgson yana ganin shugaban kungiyar Steve Parish zai damu a kan yadda kungiyar take nuna sha'awarta a kan matashin dan wasan gaba na Faransa Michael Olise, mai shekara 21, a bazaran nan. (Evening Standard)
Ana sa ran matashin dan wasan tsakiya na Arsenal Charlie Patino, dan Ingila mai shekara 19 wanda ya shafe kakar nan yana zaman aro a Blackpool, ya bar kungiyar ta Gunners a bazara. (Athletic)
Watakila ma'aikatan cibiyar horad da matasan 'yan wasa ta Chelsea su bar aiki idan har kungiyar ta Stamford Bridge ta sayar da 'yan wasanta na gida da yawa a bazara. (Times )