You are here: HomeAfricaBBC2023 05 02Article 1759472

BBC Hausa of Tuesday, 2 May 2023

    

Source: BBC

BBC ta buɗe sabuwar tashar rediyo kan rikicin Sudan

Hoton alama Hoton alama

A Talatar nan ne BBC ke ƙaddamar da wani shirin rediyo na gaggawa ga al'ummar Sudan ƙarƙashin sashen Larabci na BBC.

Za a riƙa yaɗa shirye-shiryen rediyon sau biyu a kullum tsawon watanni uku, inda za a riƙa bayar da labarai da bayanai ga al`ummar kasar da ke fama da rikici.

Zai hada da bayanan shaidun gani da ido da labaria kan ƙoƙarin da ake yi na sulhunta lamarin ta hanyar diflomasiyya, da kuma taimakawa wajen dakatar da gurɓatattun rahotanni.

Darakta janar na BBC, Tim Davie ya ce matakin na da matukar muhimmanci a lokacin da ake fuskantar rashin tabbas.

Za a watsa shirin kai tsaye daga Landan, tare da samun ƙarin bayanai daga tawagar ƴan jarida da ke ƙasashen Jordan da Masar.

Za a riƙa yaɗa shirye-shiryen ne ta mita mai gajeren zango a Sudan, inda masu saurare za su iya jin bayanai kan yadda ake samun kayan tallafi da sauran abubuwan buƙatu masu muhimmanci.

Fadan da ya ɓarke a babban birnin kasar Sudan, Khartoum, da ma wasu wurare a ƙasar, ya samo asali ne daga wata gwagwarmayar dafe madafun iko tsakanin shugabannin sojojin ƙasar.

Rikicin dai na faruwa ne a tsakanin sojojin gwamnati da kuma dakarun RSF.

Shugabar sashen yaɗa labaru a ƙasashen duniya ta BBC, Liliane Landor, ta ce "Al`amarin sudan na ƙara ta'azzara cikin sauri, inda ƴan kasar ke neman sahihan bayanai da shawarwari a daidadi lokacin da ake buƙata.

Read full article