BBC Hausa of Wednesday, 5 July 2023
Source: BBC
Shugaban Senegal Macky Sall, ya ce ba zai nemi takarar a wani wa'adi na uku ba, matakin da ke kawo karshen raɗe-raɗin da ake yaɗawa kan anniyarsa ta sake neman tazarce a zaɓen 2024.
Kundin tsarin mulkin Senegal ya bai wa mutum damar takarar shugaban kasa sau biyu kacal.
Jagoran 'yan adawa Ousmane Sonko, ya bukaci a fito zanga-zanga muddin Mista Sall ya furta anniyar neman tazarce karo na uku.
A watan da ya gabata, akalla mutum goma sha shida aka kashe a lokacin wata zanga-zanga da ta barke bayan yanke hukuncin shekara biyu a gidan yari kan Mista Sonko.
Magoya-bayansa na cewa ana yi masa bita-da-kullin siyasa.
Me ya janyo raɗe-raɗin?
Me ya sa aka yi tunanin Macky Sall wanda aka zaba a 2012 da 2019, zai sake tsayawa takara?
Wannan ita ce tambayar da ta kasance a bakin kowa na tsawon watanni.
Haka kuma shi da kansa ya taka muhimiyar rawa wajan jefa al'ummar kasar cikin zulumi a hirarrakin da ya yi da kafafen yaɗa labarai a baya.
To sai dai a jawabin da ya yi wa al'ummar kasar da aka nuna a kafar talibjin a ranar Litinin da dadare shugaba Macky Sall ya fito fili ya sanar da shawarar da ya yanke wanda ya ce, zai ba mutane da dama mamaki musaman magoya bayansa.
Ya ce "bayan na dauki tsawon lokaci ina nazari a yanzu shawarar dana yanke ita ce ba zan tsaya takara a zaɓen shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabarairun baɗi ba, duk da cewa kundin tsarin mulki ya bani damar yin haka.
"Na san shawarar dana yanke na kin tsayawa takara za ta ba mutane da dama mamaki wadanda na san cewa suna alfahari da ni kuma akwai aminci tsakanimu."
Neman hadin-kai
Shugaba Sall ya jadada bukatar ganin cewa al'ummar kasar sun haɗa kai, kuma ya nuna alhini a kan mutum 16 da suka rasa rayukansu a zanga-zangar baya-baya nan, ya na mai cewa ya na son ya kare mulkin dimokuraɗiyya kasar tare da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
To sai dai yayinda 'yan kasar da dama ke jinjina masa game da shawarar da ya yanke, wasu kuwa cewa suka yi, ya yi hakan ne domin kauce wa mumunan sakamako.
Aminata Toure, tsohuwar firaminista a gwamnatinsa wadda yanzu ta koma bangaren 'yan hammaya da ke cewa:
"Duk da cewa ba a makara ba amma kamata ya yi a ce ya mutuntuta kundin tsarin mulki.
Tun lokacin da aka sake zaɓarsa a 2019 ne ya kamata ce ya sanar da matsayinsa.
Da ya yi haka tun farko da kasar ba ta tsanci kanta a cikin halin da take ciki ba a yanzu.
Idan ba a manta ba mun rasa mutum 16 kuma ya zaman dole ga kwamitin bincike da aka dora alhaki ya faɗa mana wadanda suka shirya harin da sauransu.
A shekarar 2016 ne shugaba Macy Salla ya sa aka sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar.
A karkashin sauye-sauyen da aka yi wa kundin, duk wani shugaba ba zai tsaya takara fiye da sau biyu ba a jere.