BBC Hausa of Tuesday, 2 May 2023
Source: BBC
Kwamishinan Hukumar Zaɓe mai Zaman kanta a jihar Adamawa, wanda aka dakatar, ya ce bai yi nadamar bayyana Ai'sha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar ba a zaɓen gwamna na 2023.
Ari ya faɗi haka ne a wata tattaunawa da BBC, inda ya ce ya bi duk dokar da ta dace kafin ayyana ƴar takarar gwamnan ta jam'iyyar APC a matsayin wadda ta yi nasara.
Matakin da kwamishinan zaɓen na jihar Adamawa ya ɗauka a lokacin zaɓen na jihar Adamawa ya janyo ruɗani, bayan da ya bayyana Binani a matsayin wadda ta yi nasara duk kuwa da cewa ba a kammala tattara sakamakon zaɓen ba.
Lamarin ya sanya Hukumar Zaɓe ta INEC ta dakatar da Ari, yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin yin bincike a kan shi da kuma jami'an tsaron da suka ba shi kariya a lokacin da abin ya faru.
A tattaunawar tasa da BBC, Ari ya ce "ni na gaya maka babu nadama, abin da za ka yi bisa doka da oda ai babu nadama."
Haka nan kuma, Barista Hudu Ari ya musanta zargin da ake yi cewa ya karɓi cin hanci na Naira biliyan biyu domin ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasara a zaɓen.
Binani dai ita ce ƴar takarar gwamna ta jam'iyyar APC a jihar Adamawa a zaɓen 2023.
Ta kalubalanci gwamna mai ci na jam'iyar PDP, Ahmadu Umaru Fintiri wanda a ƙarshe hukumar zaɓen ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen a wa'adi na biyu.
Barrister Hudu Yunusa, wanda rundunar ƴan sanda ke nema, ya ce doka ce ta ba shi hurumin sanar da sakamakon.
Ya ƙara da cewa a shirye yake ya miƙa kansa ga rundunar ƴan sandan Najeriya da ke neman sa nan ba da jimawa ba.
Za ku iya kallon bidiyon tattaunawar a ɓangaren bidiyo na shafinmu da kuma shafukanmu na sada zumunta.