You are here: HomeAfricaBBC2021 07 13Article 1307575

BBC Hausa of Tuesday, 13 July 2021

    

Source: BBC

Barca ta fara atisayen tunkarar kakar 2021/22 ran Litinin

Yan wasan kungiyar Barcelona a training Yan wasan kungiyar Barcelona a training

Barcelona ta fara atisayen tunkarar kakar tamaula ta 2021/22 ranar Litinin, bayan da ta kammala auna koshin lafiyar wasu 'yan wasanta a Ciutat Esportiva.

Cikin fitattun 'yan wasan da suka motsa jiki a Barca sun hada da Dest da Pique da Pjanic da Riqui Puig da Neto da S. Roberto da kuma Umtiti.

Sauran sun hada da Inaki Pena da Arnau Tenas da Álex Collado da Gavi da Comas da Nico da kuma Yusuf Demir.

Sai dai dan kwallon Brazil, Philippe Coutinho ya yi atisayensa shi kadai a kokarin da yake na murmurewa daga raunin da ya yi tun kan kammala kakar da ta wuce.

Ronald Koeman ne ya ja ragamar atisayen duk da cewar wasu 'yan wasan na hutu, bayan da suka buga Copa America da wadanda suka fafata a Euro 2020.

Sai dai kuma Pedri da Eric Garcia da kuma Oscar Mingueza za su wakilci Sifaniya a gasar kwallon kafa da za a yi a Tokyo daga watan gobe.

Tun kafin fara atisayen a ranar Litinin sai da shugaban kungiyar, Joan Laporta ya ziyarci 'yan wasan a Ciutat Esportiva.

Barcelona za ta yi wasan sada zumunta na farko da Gimnàstic de Tarragona ranar 21 ga watan Yuli a filin wasa na Johan Cruyff.

A dai filin za ta fafata da Girona ranar Asabar 24 ga watan Yulin 2021.

Read full article