BBC Hausa of Monday, 4 September 2023
Source: BBC
Kungiyar Barcelona za ta buga wasa biyar cikin watan Satumba da ya kunshi karawa hudu a La Liga da daya a Champions League.
Cikin watan Agusta, Barcelona ta ci wasa biyu da canjaras daya a fafatawa ukun da ta buga a La Liga na bana, wadda ita ce ke riƙe da kofin bara.
Cikin wasa huɗun da za ta kara a cikin watan Satumba za ta yi gumurzu biyu a gida da biyu a waje har da wanda ta ziyarci Osasuna ranar Lahadi 2 ga watan Satumba.
Daga nan za a yi hutu, sannan a koma fagen fama, inda Barcelona za ta karɓi baƙuncin Real Betis, sannan ta ƙara yin wasa a gida da Celta Vigo a dai La Liga.
Ranar 27 ga watan Satumba, Barcelona za ta ziyarci Real Mallorca, domin buga karawa ta huɗu da za ta yi a cikin watan Satumba.
Barcelona za ta fara wasan farko a cikin rukuni a Champions League da Royal Antwerp ranar 19 ga watan Satumba, rabon da ta ɗauki kofin tun 2014/15 mai biyar jimilla.
Ƙungiyar Sifaniya tana rukuni na takwwas da ya hada da FC Porto da kuma Shakhtar, waɗanda za ta fuskanta a cikin watan Oktoba.
Manchester City ce ke riƙe da Champions League, wanda ta lashe a bara bayan doke Inter Milan.