You are here: HomeAfricaBBC2022 06 13Article 1559249

BBC Hausa of Monday, 13 June 2022

    

Source: BBC

Batun zabar mataimakan 'yan takarar shugaban kasa ya zama alakakai a Najeriya

Hagu zuwa dama: Atiku Abubakar, Rabiu Musah Kwankwaso, Peter Obi da Bola Tinubu Hagu zuwa dama: Atiku Abubakar, Rabiu Musah Kwankwaso, Peter Obi da Bola Tinubu

Ga alama dai manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya na cikin tsaka-mai-wuya wajen fitar da wanda zai zamo wa 'yan takarar shugaban kasa mataimaki bayan kammala zabukan fitar da gwani na shugaban kasa.

An shafe ƙarshen makon jiya, ana tattaunawa da tuntuɓa tsakanin ƙusoshin jam'iyyun siyasar Najeriyar a ƙoƙarinsu na fitar da mataimakan 'yan takararsu na shugaban ƙasa.

Tuni dai ake ta ce-ce-ku-ce game da addinin da ya kamata jam'iyyun su yi la'akari da shi wajen fitar da mataimakan.

Idan aka yi la'akari da wanda ya samu takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulkin kasar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya kasance Musulmi daga kudu, wanda ake gani dauko mataimaki daga arewa zai zamo mishi babban kalubale.

Batun Kirista ko Musulmi zai dauka, ya zamo babban abin muhawara a tsakanin al'ummar Najeriyar.

Akwai dai rahotanni da suka ambato manyan arewacin kasar na masa hannunka mai sanda a kan cewa daukar Musulmi mataimaki zai fi ba shi damar samun nasara musamman a yankin, a inda Kiristoci kuma ke cewa hakan ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa.

Kafofin yada labarai sun ambato shugaban kungiyar Kiristoci ta CAN, a Najeriya Dakta Samson Ayokunle, na gargadin cewa daukar mataimaki Musulmi ga dan takara Musulmi, mataki ne da ka iya zama tamkar wani bala'i ga kasar.

Wani dan majalisar wakilai a jam'iyyar APC, Honourable Yusuf Adamu Gaddi, ya ce matakin ba abin lamunta ba ne.

Ya ce,"Idan ka duba yanayin da kasarmu ke ciki ana bukatar juna a gudu tare a tsira tare, don haka duk mai son zaman lafiya dole ya yi tunanin raba dai dai, ma'ana idan an ba mu wannan a ba ku wancan."

Idan Musulmi ne shugaban kasar Najeriya, to ya kamata Kirista ya yi mishi mataimaki don a zauna lafiya in ji dan majalisar.

Shi kuwa Ibrahim Kabir Masari, kusa a jam'iyyar APC, cewa ya yi batun mutumin da zai kasance mataimakin shugaban kasa ga dan takararsu, hurumi ne da Bola Ahmed Tinubu, ya bar wa Shugaba Muhammadu Buhari.

A nata bangaren, babbar jam'iyyar adawar Najeriyar PDP kuwa ta ce dan takarar shugaban kasarta Atiku Abubakar, na dab da kammala tuntuba don dauko mataimaki Kirista daga yankin kudu maso kudu ko kuma kudu maso gabashin kasar.

Mataimakin sakataren yada labarai na kasa a jam'iyyar ta PDP, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa BBC cewa, ba sa tunanin dauko mataimakin shugaban kasa daga yankin kudu maso yamma wato bangaren Yarabawa, saboda su sun riga sun taba rike kujerar shugaban kasar a lokacin Obasanjo, ga shi kuma a yanzu dan takarar shugaban kasa a APC ma daga can ya fito.

Ya ce don haka yanzu suna duba wasu wanda suma 'yan Najeriya ne da ke da hakkin wannan kujerar, kamar Gwamnan Rivers Wike da Gwamnan Delta da na Akwa Ibom da ma wasu sanatoci a yankin da suke gani za su zabi mataimaki daga cikinsu.

A wasu jam'iyyun dai tuni maganar dauko dan takarar mataimakin shugaban kasa ta fada.

Read full article