BBC Hausa of Monday, 5 June 2023
Source: BBC
Fitaccen ɗan wasan gaban Real Madrid Karim Benzema zai bar ƙungiyar bayan shafe shekara 14 a Santiago Bernabéu.
Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or a shekarar da ta wuce, ya fara taka leda ne a Madrid a shekarar 2009 bayan da ƙungiyar ta ɗauke shi daga Lyon.
Benzema mai shekara 35 zai bar Real Madrid ne bayan da kwantiraginsa da ƙungiyar ya zo ƙarshe a kakar da muke ciki.
Benzema ya ci manyan kofuna 25 a tsawon shekaru 14 da ya yi a ƙungiyar, ciki har da kofunan Gasar Zakarun Turai na Champions Leagues biyar, tare da kofunan Laliga huɗu.
Ƙungiyar Real Madrid ta ce ''Benzema zaƙaƙurin ɗan wasa ne mai kyakkaywar mu'amala, kuma ya ɗaga martabar ƙungiyarmu, dan haka yana da damar fayyace makomarsa''.
Dan wasan ya buga wa Real Madrid wasa 647, ya kuma zira ƙwallaye 353, shi ne ɗan wasa na biyu da ya fi ci wa ƙungiyar ƙwallo bayan Cristiano Ronaldo.
Ana sa ran wasansa na ƙarshe a ƙungiyar shi ne wanda Real Madrid za ta kara da Athletic Bilbao a yau Lahadi a wasan ƙarshe na gasar Laliga ta kakar bana.
Ana rade-radin cewar ɗan wasan zai koma taka-leda a ƙasar Saudiyya bayan da ya samu tayi mai gwaɓi daga wata ƙungiya a ƙasar.
Idan ta tabbata, ɗan ƙwallon zai haɗe da tsohon abokin wasansa Cristiano Ronaldo a Saudiyya amma a matsayin abokin hamayya.