You are here: HomeAfricaBBC2021 07 01Article 1299517

BBC Hausa of Thursday, 1 July 2021

    

Source: BBC

Bill Cosby: An sako shaharren dan wasan barkwancin bayan kotu ta wanke shi

Bill Cosby, shahararen dan wasan barkwanci Bill Cosby, shahararen dan wasan barkwanci

Ɗan wasan barkwancin ya bar gidan kaso bayan da kotun kolin jihar Pennsylvania ta wanke shi daga aikata laifin cin zarafin wata mata.

Alkalan kotun sun ce masu shigar da kara ba su bi ƙa'ida ba, amma sun amince cewa hukuncin nasu zai bayar da mamaki.

Mista Cosby mai shekara 81 da haihuwa ya shafe fiye da shekara biyu cikin shekara 10 da kotu ta daure shi a wani gidan yarin jiha da ke kusa da birnin Philadelphia.

A 2018 aka same shi da laifin saka wa wata mata mai suna Andrea Constand, wadda ƴar wasan kwallon kwando ce, abin maye da kuma cin zarafin ta.

Mista Cosby ya shahara ne sanadiyyar wani wasan barkwanci na talabijin da ya dade yana fitowa a ciki mai suna The Cosby Show a shekarun 1980.

Akwai gomman mata da suka sha yin zarge-zarge a bainar jama'a cewa Mista Cosby ya ci zarafinsu, amma a kan lamarin Andrea Constand ne kawai aka taba yi ma sa shari'a.

A hukuncin da kotun ƙolin jihar Pennsylvania ta yanke ranar Laraba, alƙalan sun ce masu shigar da ƙara ba su bi ƙa'ida ba saboda lauyoyin Mista Cosby sun kulla wata yarjejeniya da tsohon mai shigar da ƙara na jihar cewa ba za a shigar da wannan ƙarar a kotu ba.

Jim kadan bayan sakinsa daga kurkuku, tsohon dan wasan talabijin din ya isa kofar gidansa, kuma da alama ya galabaita. Bai ce komai ga manema labaran da ke jiransa ba, amma lauyoyinsa da kakakinsa ne su ka yi magana a madadinsa.

Read full article