You are here: HomeAfricaBBC2021 06 23Article 1292926

BBC Hausa of Wednesday, 23 June 2021

    

Source: BBC

Chelsea da Man City na takara kan Grealish, Mbappe ya nemi izinin barin PSG

Jack Grealish, dan kwallon tawagar Ingila mai taka leda a Aston Villa Jack Grealish, dan kwallon tawagar Ingila mai taka leda a Aston Villa

Chelsea ta shirya yin takara da Manchester City wajen daukar dan kwallon tawagar Ingila mai taka leda a Aston Villa, Jack Grealish, 25. (Football Insider)

Dan wasan tawagar Faransa, Kylian Mbappe ya nemi izinin barin Paris St Germain. Yarjejeniyar dan wasan mai shekara 22 za ta kare a kungiyar a karshen kakar badi. (Marca, via Daniel Riolo of RMC Sport)

Dan wasan Manchester City, Raheem Sterling ba zai so a yi musaya da shi ba zuwa Tottenham, ita kuma ta bai wa kungiyar Etihad Harry Kane mai shekara 27 ba. (ESPN)

Chelsea za ta yi kokarin daukar dan wasan tawagar Sifaniya mai taka leda a Villareal, Gerard Moreno mai shekara 29, idan har ba za a sayar mata da dan kwallon tawagar Norway, Erling Braut Haaland, mai shekara 20, daga Borussia Dortmund. (Fichajes, via Mirror)

Mai tsaron bayan Sifaniya, Sergio Ramos, mai shekara 35, ba zai amince da tayin da Manchester United da Manchester City za suyi masa zai kuma koma taka leda a Paris St-Germain da zarar yarjejeniyarsa ta kara a Real Madrid a karshen watan nan. (AS)

Watakila Arsenal ta sayar da dan wasan tawagar Faransa William Saliba, bayan da ta ke daf da daukar dan wasan Brighton mai tsaron bayan tawagar Ingila, Ben White, mai shekara 23. (Football London)

Kungiyar Wolves da ta West Ham na son daukar dan kwallon Burnley mai tsaron bayan Ingila, James Tarkowski, mai shekara 28, wanda zai shiga kakar karshe a yarjejeniyarsa a Turf Moor. (Telegraph - subscription required)

Kungiyoyin Brighton da Burnley da Newcastle United da kuma Southampton na son yin zawarcin mai tsaron bayan Liverpool, Nathaniel Phillips. (Goal)

Newcastle na son tsawaita kwantiragin dan kwallon tawagar Ingila, Jacob Murphy, wanda saura kaka daya ta rage masa a kungiyar, kuma kungiyoyi da dama na son sayen dan wasan mai shekara 26. (Sky Sports)

Norwich na fatan daukar aron dan wasa mai shekara 20 dan kwallon tawagar Scotland mai wasa daga tsakiya, Billy Gilmour daga Chelsea. (Mail)

Read full article