BBC Hausa of Sunday, 17 September 2023
Source: BBC
Bournemouth da Chelsea sun tashi ba ci a wasan mako na biyar a gasar Premier da suka kara a Vitality ranar Asabar.
Wannan shi ne wasan farko da aka tashi ba ci a babbar gasar tamaula ta bana tun da aka fara ranar 11 ga watan Agustan 2023.
Har yanzu Bournemouth ba ta ci wasa ba a kakar nan karkashin koci, Andoni Iraola, shi kuwa Mauricio Pochettino karawa ɗaya ya ci daga fafatawa biyar.
Chelsea ta samu damar makin cin kwllo ta hannun Nicolas Jackson da Raheem Sterling da ya buga kwallo ta bugi turki.
Shi kuwa Levi Colwill ya buga kwallo ta shiga raga, amma daga baya aka soke da cewar an yi satar gida.
Sabon dan wasan da Chelsea ta ɗauka, Cole Palmer ya kusan cin kwallo, sai dai da ya buga ta nufi kai tsaye wajen Nato.
Ita ma Bournemouth ta samu tata damar makin to amma bai kai wanda kungiyar Stamford Bridge ta samu ba.
Chelsea wadda ta kashe makudan kuɗi wajen sayo 'yan wasa ta yi sauye-sauye da yawa a karawar, yayin da Conor Gallagher ne ya ɗaura kyallen kyaftin.
Ɗan wasan da Chelsea ta saya a bana mai tsada sama da fam miliyan 100, Moises Caicedo bai buga fafatawar ba, saboda jinya da yake yi.
Ɗan kwallon ya ji ciwo lokacin da ya je ya buga wa Ecuador wasa biyu da ta buga a neman shiga gasar kofin duniya.
Ranar 2 ga watan Satumba, Nottingham Forest ta ci Chelsea 1-0 a Stamford Bridge a wasan mako na huɗu a Premier League.