You are here: HomeAfricaBBC2023 04 03Article 1743125

BBC Hausa of Monday, 3 April 2023

    

Source: BBC

Chelsea ta tafi farautar Nagelsmann, Leicester na Nazari kan Potter

Tsohon kocin Bayern Munich Julian Nagelsmann Tsohon kocin Bayern Munich Julian Nagelsmann

Rafael Benitez da Jesse Marsch da Ralph Hasenhuttl da Adi Hutter dukka na fafutikar maye gurbin koci a Leicester City. (Mail)

Korar Graham Potter da Chelsea ta yi ya kwadaita Leicester City, kocin ya kasance wanda ake ganin dama ana son ya maye gurbin Brendan Rodgers. (Leicester Mercury)

Potter na iya samun damar komawa Leicester City gadan-gadan. (Talksport)

Kocin Fulham Marco Silva ya kasance mutumin da Chelsea ke son bai wa aikin koci. (Mirror)

Chelsea tana kuma nuna sha'awarta kan dauko tsohon kocin Bayern Munich Julian Nagelsmann bayan korar Potter, akwai kuma tsohon koci Mauricio Pochettino da shi me ke kan layi. (Talksport)

Tuni dai aka tuntubi Nagelsmann da tayin zama sabon kocin Chelsea. (Fabrizio Romano)

Sai dai, Nagelsmann ba ya sha'awar maye gurbin Potter a Chelsea. (Sky Sports Germany, via Mirror)

Liverpool na zawarcin dan wasan Chelsea da Ingila Conor Gallagher, mai shekara 23. (Independent)

Arsenal na harin 'yan wasa uku a sabuwar kaka, da suka hada da mai taka leda a Everton da Belgium Amadou Onana, da dan wasan Brighton da Ecuador Moises Caicedo, da kuma mai bugawa West Ham da Ingila Declan Rice. (Football Insider)

Newcastle United ta matsu ta saye dan wasan Leicester City da Ingila James Maddison, mai shekara 26. (Football Insider)

Chelsea na Nazari kan dan wasan da Real Madrid ke kwadayi, Reece James mai shekara 23, tana iya bukatar fam miliyan 90 a kan sa. (Football Insider)

Ana ganin Aston Villa za ta fi dacewa da dan wasan Southampton da Ghana Mohammed Salisu, maimakon ya tafi Chelsea ko Manchester United. (GiveMeSport)

Liverpool na zawarcin dan wasan Eintracht Frankfurt Jesper Lindstrom, mai shekara 23, amma tana fuskantar kalubale daga Arsenal. (Florian Plettenberg - Sky Sports Germany)

Kungiyoyin firimiya na sa ido kan dan wasan Koriya ta Kudu Lee Kang-in, mai shekara 22, da ake tunanin ya bar Mallorca a wannan kaka. (Fabrizio Romano)

Read full article