You are here: HomeAfricaBBC2021 08 01Article 1322083

BBC Hausa of Sunday, 1 August 2021

    

Source: BBC

Cutar koron : Ana duba yiwuwar sake kafa dokar kulle a wasu yankunan a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Mahukunta a Najeriyar sun yi gargadin cewa kasar ta fara shiga mataki na uku na annobar korona a dan tsakanin nan, har ma an sami kimanin mutum goma da suka kamu da sabon nau'in annobar.

Sai dai sun ce, ana ci gaba da bin dukkan matakan da suka kamata don ganin an dakile yaduwarta.

Wani jami'i a kwamitin shugaban Najeriya da ke yaki da annobar korona Dakta Muktar Muhammed, ya shaida wa BBC Hausa cewa yanzu haka mahukunta na duba yiwuwar sake kafa dokar kulle a wasu yankuna da cutar ta fi yaɗuwa, sai dai a wanan karon ba za ta kasance ta bai ɗaya ba, a maimakon hakan za a yi duba da inda aka fi samun yaɗuwar cutar ne a jihohi da ma tarayya baki ɗaya.

A cewarsa, ''A gaskiya a kwanakin baya mun ga cewa anobar ta ja baya, domin ba a samun masu kamuwa da cutar sosai, to amma yanzu yawan ya karu, saboda mutane sun daina daukar matakan kariya, don haka ba abun mamaki bane idan yawan ya karu ayanzu''.

Ya ce zuwa yanzu an gano mutanen da suka kamu da cutar nau'in Delta akalla goma sha wani abu, ''Don haka lallai hakika akwai wannan nau'u a Najeriya kuma yana dada karuwa, muna ma zargin cewa za a iya danganta karuwar masu kamuwa da cutar da shi wannan nau'i a yanzu haka.

Yaya nau'in delta yake?

Ba wani sabon abu ba ne idan kwayar cutar bairos ta hayayyafa da sauya tsarin halittarta a yayin da take yaduwa, kuma tuni masana kimiyya suka yi gargadin cewa wasu nau'ukan masu ban tsoro za su iya bijirowa.

Ko da yake har yanzu ba a kai ga sanin yadda yake yaduwa ba, amma bincike ya nuna cewa nau'in na delta yana da karin hatsari da ke tattare da yadda yake yaduwa cikin sauri.

A watan Mayu Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ayyana nau'in na delta a matsayin "nau'in da ya kamata ya sanya damuwa".

Ana ayyana nau'in bairos a matsayin wanda ya kamata a damu da shi sosai ne idan akwai karin shaidu da ke nuna cewa nau'in ya fi saurin yaduwa, yana kuma haifar da cutuka masu zafi sannan yana rage karfin tasirin riga-kafi da magunguna.

Shin nau'in delta na haddasa karin cutuka masu zafi ko alamominsu?

Ana bukatar gudanar da karin bincike kan nau'in na delta, amma akwai alamu da ke nuna cewa nau'in na delta yana iya haddasa cutuka masu zafin gaske.

Wani bincike da aka wallafa a mujallar kimiyya ta The Lancet ranar 14 ga watan Yuni ya yi nazari kan tasirin nau'in delta a Scotland, inda ya mamaye.

Masu bincike sun gano cewa kasadar kwantar da mutumin da ya kamu da nau'in delta na cutar korona ta ninka idan aka kwatanta da wanda ya kamu da nau'in alpha.

Kazalika masu bincike a Birtaniya sun gano cutar korona nau'in delta take da alamomi daban da na nau'in da aka fi sani.

Bayanai sun nuna cewa masu fama da nau'in delta suna nuna alamomin da suka hada da ciwon kai, bushewar makogwaro, majina da kuma zazzabi — irin wanda mutumin da ya kamu da mura yake fama da shi.

Read full article