BBC Hausa of Thursday, 25 May 2023
Source: BBC
Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ta kare matakin da ta dauka na ciwo basussuka masu dimbin yawa a ciki da wajen kasar a shekaru takwas da ta shafe ta na mulki.
Basussukan da kasar ta ciyo ya sa wasu 'yan Najeriya da masana tattalin arziki sun nuna damuwa a kan matsalolin da kasar za ta iya fuskanta sakamakon yawan basussukan.
Sai dai ministar kudi da tsare-tsaren tattalin arziki ta kasa ta Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmed ta shaidawa BBC cewa gwamnati ta karɓo bashin ne domin hana kasar faɗawa cikin mawuyacin hali a lokacin da kasar ta samu koma bayan tattalin arziki a shekarun 2016 da 2020.
"Mun samu durkushewar tattalin arzikin kasa sau biyu, a 2016 da 2020 lokacin annobar korona, mun yi iya kokarinmu wajan ganin ƙasar ba ta faɗa cikin mawuyacin hali ba".
"Saboda kasa mai girma irin Najeriya idan aka barta cikin wannan hali, abin zai baci ne, nesa ba kusa ba", in ji ta.
'Mun rage dogaro kan man fetur'
Ministar ta kuma kara da cewa a lokacin da suka karɓi ragamar mulki a shekarar 2015 kasafin kuɗin kasar ya kai naira tiriliyan 4.5 amma a wannan shekarar kasafin kuɗin kasar ya kai naira triliyan 21.5
A cewarta bayan gyaran da suka yi wa kasafin kuɗi daga watan Janairu zuwa Disamba sun kuma aiwatar da wasu tsare-tsare domin tabbatar da adalci wajen aiwatar da kasafin kudi:
"Mun shigo da hanyar gyara hanyoyin da ke barin ana barbar kudin, kuma wadannan mun yi su ne ta cikin tsarin shari'a da ake kira 'finance bill'."
"Sun taimaka mana mun samu karin kuɗin shiga wa gwamnatin tarayya, daga tiriliyan 3 zuwa tiriliyan 10.7 a bara''.
Zainab Shamsuna ta kuma ce gwamnati ta sauya fasalin kuin da ke shigowa.
A cewarta da farko kashi 70 cikin 100 na kasafin kuɗin kasar ya dogara ne a kan man fetur amma a yanzu kashi 65 cikin 100 na kasafin kuɗin ana samunsa ne daga ɓangaren da ba na man fetur ba.
Ministar ta kuma ce dukushewar tattalin arzikin da aka samu a lokacin bullar annobar korona ta sa gwamnati sake ciyo bashi
Sai dai a karkashin mulkin shugaba Buhari ne aka samu tashin farashin kayayyaki da faɗuwar darajar naira da kuma ta karawa kasa dimbin bashi ko da yake ministar ta kare matakin.
"Ba mu ne ka dai mu ke da bashi ba, ba bu kasar da bata neman bashi, mun kuma sami shugaban kasa da yake cewa ku amsa domin ayi manyan ayuika’’.
Game da tashin farashin kayayaki kuwa ministar ta ce ba Najeriya ka dai bace matsalar ta shafa.
A cewarta matsalar nada nasaba da yakin Ukraine da kuma annobar korona.