You are here: HomeAfricaBBC2021 08 16Article 1334410

BBC Hausa of Monday, 16 August 2021

    

Source: BBC

Dan wasan Chelsea Tammy Abraham zai koma Roma kan fam miliyan 34

Dan wasan Chelsea, Tammy Abraham Dan wasan Chelsea, Tammy Abraham

Dan wasan Chelsea, Tammy Abraham ya je Italiya ranar Lahadi a shirin da yake na komawa Roma da taka leda kan fam miliyan 34.

Wakilan dan wasan tawagar Ingila sun cimma yarjejeniya tsakanin kungiyoyin biyu a karshen mako.

Ranar Lahadi Chelsea ta kammala cinikin Romelu Lukaku daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5.

Shine dan wasan da ta dauka mafi tsada a tarihi, kuma na biyu da aka saya da kudi mai tsoka a Burtaniya, bayan Jack Grealish daga Aston Villa.

Manchester City ce ta dauki Grealish dan kwallon tawagar Ingila kan fam miliyan 100 a bana a matakin wanda aka saya mafi tsada a Burtaniya kuma na tara a duniya.

Idan Abraham ya taka rawar gani a Roma, cinikin zai kai fam miliyan 68 nan gaba.

Amma hakan ba zai yiwuba har sai bayan kaka biyu idan ya taka rawar gani a kungiyar da Jose Mourinho ke jan ragama.

Read full article