BBC Hausa of Monday, 12 June 2023
Source: BBC
Novak Djokovic ya zama zakaran French Open na bana, bayan da ya doke Casper Ruud ranar Lahadi.
Djokovic, mai shekara 36, ya yi nasarar ne da ci 7-6 (7-1) 6-3 7-5 a wasan da suka buga a birnin Paris.
Dan ƙasar Serbia ya lashe manyan kofin kwallon tennis na 23, ya sha gaban Rafael Nadal mai 22 jimilla.
Ya zama na farko da ya ɗauki manyan kofi huɗu a kaka ɗaya karo na uku yana wannan bajintar.
Da wannan nasarar ta sa Djokovic ya yi kan-kan-kan da Serena Williams a yawan lashe manyan kofunan tennis, wadda take kan gaba a wannan kwazon ita ce Margaret Court mai 24.
Watakila ɗan ƙasar Serbia ya ɗauki na 24 a Wimbledon Open da za a yi a watan gobe, gasar da ya lashe karo bakwai.
Djokovic, wanda zai koma mataki na ɗaya a jerin masu buga tennis a duniya, ya faɗi a fili don murna a lokacin da ya lashe kofin bana.