BBC Hausa of Friday, 23 June 2023
Source: BBC
Ana ci gaba da aikawa da sakon ta'aziyya da alhini daga sassan duniya, kan mutuwar mutane biyar da ke cikin jirgin ruwan nan na karkashin teku da ya bace a arewacin tekun Atalantika a Amurka.
Tun a ranar Lahadi ne jirgin na sunduki ya kama hanyarsa ta zuwa karkashin teku inda mataccen katafaren jirgin ruwan nan na Titanic wanda ya yi hadari a shekarun 1912 yake a karkashin teku.
Mutanen biyar wadanda sun hada da shugaban kamfanin jirgin ruwan, da wasu 'ya Birtaniya yan asalin Pakistan biyu, da dan asalin Birtaniya daya, da Bafaranshe guda za su je yawon bude idanu ne, inda jirgin ya bace aka shiga gagarumin nema tsawon kwana biyar.
Hukumomin sojin ruwan Amurka sun ce ‘yan sa’o’i da fara tafiyar jirgin ruwan nan na sunduki mai tafiya a karkashin teku wanda ya yi hadari an ji wata kara ta kama da fashewa.
Suka ce tun daga nan ne suka mika bayanin karar ga jamian tsaron gabar teku na Amurkar, wanda hakan ya sa a ka takaita fadin yankin da ake neman jirgin ruwan, wanda ya yii hadarin da ya hallaka dukkanin mutane biyar da ke cikinsa.
An shaida wa kafafen watsa labaran Amurka cewa an jiyo wasu sautukan gagarumar fashewa da suka yi daidai da tarwatsewar jirgin bayan ya yi ninkaya cikin tekun ya kama hanyarsa ta zuwa inda ya nufa tun a ranar Lahadi.
Jami'an tsaron gabar tekun Amurka sun ce wata mummunar fashewa ta hallaka dukkan mutane biyar da suka bace a jirgin ruwan nan na Titanic.
Wani abu da ba a fayyace ba shi ne duk da wannan bayani da hukumar sojin ruwan ta Amurka ta bayar na jin wannan kara tun da farkon farin tafiyar jirgin wanda rashin jin duriyarsa da kuma sanin halin da yake ciki ya tayar da hankali aka shiga gagarumin aikin nema da ceto, shi ne mai ya sa ba a bayyana wannan magana ba tun da farko ta jin alamun karar fashewar?
An dai yi amanna cewa wannan kara da aka ji wata na’ura ce ta musamman ta sirri ta sojin ruwan na Amurka ta jiyo ta, na’urar da ake da ita tun lokacin yakin cacar baka.
Wadda aka kirkira tun shekarun 1950 domin satar jin motsin jirgin ruwa na karkashin teku na Rasha a can cikin tekun Atalantika.
Yanzu dai fadar gwamnatin Amurka, White House ta fitar da sanarwa a kan mutunen biyar da suka mutu a wannan jirgin ruwa na sunduki na karkashin teku.
Sanarwar da a ciki take nuna alhini na rashin mutanen tare da ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwansu.
Sanarwar ta kuma yi godiya ga jami’ai da kasashen da suka shiga wannan gagarumin aiki na neman jirgin.
A jiya Alhamis ne wata na’urar da wani jirgin ruwan Canada ya saka a cikin tekun ya gano wasu tarkace na jirgin har guda biyar abin da ya tabbatar da cewa jirgin ya tarwatse ne da mutanen biyar da ke ciki.
Na’urar ta gano tarkacen jirgin ne a karkashin tekun na Atalantika a wajen da ke da nisan kafa 1,600 daga inda mataccen katafaren jirgin ruwan nan na Titanic wanda mutanen biyar za su je wajensa yake a cikin tekun.
Iyalan mutanen biyar sun fitar da sanarwa inda suka ce suna samun ta’aziyya daga sassan duniya daban-daban.