BBC Hausa of Wednesday, 7 December 2022
Source: BBC
Eden Hazard ya yi ritaya daga buga wa tawagar Belgium tamaula yana da shekara 31, bayan da aka fitar da kasar daga Gasar Kofin Duniya a Qatar.
Hazard ya fara yi wa kasar tamaula yana da shekara 17 da haihuwa a 2008, wanda ya yi karawa 126 da cin kwallo 33.
Dan wasan yana cikin tawagar Belgium da ta kai daf da karshe a Gasar Kofin Duniya a 2018, inda Faransa ta doke ta 1-0.
Sai dai Belgium ita ce ta uku a wasannin, bayan da ta yi nasara a kan Ingila.
Hazard ya fara buga wa Belgium wasa a karawa da Luxembourg, wanda ya shiga canji - a lokacin shi ne matashi na takwas da ya yi wa kasar tamaula.
Daga nan ya buga wasa uku a Gasar Kofin Duniya da karawa biyu a Gasar nahiyar Turai - wanda ya yi wa kasar kyaftin sau 56.
Hazard ya buga wasannin Gasar Kofin Duniya uku a Qatar, inda Belgium ta ci Canada 1-0, sannan ta tashi 0-0 da Croatia, sannan Morocco ta doke ta 2-0.
Tsohon dan wasan Chelsea ya koma Real Madrid kan £150m a 2019.
Ya yi kaka bakwai a Stamford Bridge da cin Premier biyu da FA Cup da League Cup da kuma Europa League.