You are here: HomeAfricaBBC2023 07 13Article 1803890

BBC Hausa of Thursday, 13 July 2023

    

Source: BBC

Everton ta dauki Ashley Young

Ashley Young Ashley Young

Everton ta kulla yarjejeniya da Ashley Young kan kwantiragin shekara daya bayan ya bar Aston Villa a bazara.

Dan wasan, mai shekaru 38, ya zama ɗan wasa na farko da Everton ta saya a ƙarƙashin kocinta Sean Dyche kuma har ya riga ya haɗe da sauran 'yan wasan ƙungiyar a sansanin da suke shirin tunkarar kakar wasa ta bana a kasar Switzerland.

An fahimci cewa Young ya fara tattaunawa da Luton kuma wadansu ƙungiyoyi a Saudiyya sun nuna sha'awarsu, amma daga baya ya yanke shawarar komawa Everton.

Mai tsaron bayan ya lashe gasar Europa da League Cup tare da Manchester United kuma ya buga wa Ingila wasanni 39, inda ya buga wasa a gasar cin kofin duniya ta 2018 da Croatia ta doke su a wasan kusa da na ƙarshe.

Young ya buga wasanni sama da 700 a kulob da kuma ƙasa, ciki har da wasanni 32 da ya buga wa Villa a kakar wasan da ta wuce, kuma zai kai kwarewarsa kungiyar Everton da ta tsallake rijiya da baya a kakar wasanni biyu da suka gabata.

Read full article