BBC Hausa of Friday, 19 May 2023
Source: BBC
Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta babbatar da wadanda zai busa wasan karshe a FA Cup tsakanin kungiyoyin Manchester a watan Yuni.
Paul Tierney ne zai busa wasan hamayya tsakanin Manchester United da Manchester City da za su kara a Wembley ranar 3 ga watan Yuni.
Tierney shine zai ja ragamar mutum bakwai da za su yi alkalancin karawar farko da kungiyoyin za su yi a wasan karshe a FA Cup.
City ta kwao wannan matakin bayan da ta ci Sheffield United 3-0 a wasan daf da karshe ranar 22 ga watan Afirilu.
United kuwa doke Brigton 7-6 ta yi a nugun fenariti, bayan da suka tashi 0-0 ranar 23 ga watan Afirilu.
United tana da FA 12, ita kuwa City tana da shida, bayan da Arsenal ce kan gaba a yawan lashe kofin mai 14 jimilla.
Alkalin, wanda ya busa wa United karawa hudu a bana, yana da kwarewa a alkalancin wasan karshe a FA Cup, wanda ya yi mataimaki a 2010 a wasan Chelsea da Portsmouth.
Wadanda za su rike labule sun hada da Neil Davies da Scott Ledger da mai jiran ko-ta-kwana, yayin da Peter Bankes ne alkali na hudu.
David Coote ne zai kula da VAR, yayin da Simon Long zai taimaka masa.
Alkalan da za su busa wasan karshe a FA Cup na 2023
Alkali: Paul Tierney
Mataimaka: Neil Davies da Scott Ledger
Alkali na hudu: Peter Bankes
Mai jiran ko-ta-kwana: Adrian Holmes
Mai kula da VAR: David Coote
Mataimakin mai kula da VAR: Simon Long