BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023
Source: BBC
Erik ten Hag ya ce watakila Antony ya murmure ya buga wa Manchester United wasan karshe a FA Cup na bana in ji Erik ten Hag.
Dan kwallon Brazil ya ji rauni a karawa a kwantan wasan Premier League da United ta ci 4-1 ranar Alhamis.
An fitar da dan wasan daga filin tamaula a kan gadon marasa lafiya yana ta sharbar kuka.
United za ta kece raini da Manchester City a Wembley ranar 3 ga watan Yuni.
United face Manchester City at Wembley on 3 June.
Antony, mai shekara 23 ya ci kwallo takwas ya kuma bayar da uku aka zura a raga, tun bayan da ya koma Old Trafford daga Ajax a cikin Satumba kan £81m.
Dan kwallon bai yi Ajax wasa takwas na karshe a kungiyar a 2021, bayan da ya ji rauni a lokacin buga wa Brazil wasan shiga kofin duniya a Maris din 2022.