BBC Hausa of Thursday, 16 November 2023
Source: BBC
Hukumar ƙwallon ƙafar Ingila ta tuhumi kocin Arsenal Mikel Arteta kan kalaman da ya yi bayan da Newcastle ta doke su da ci 1-0.
Arteta, mai shekaru 41, ya bayyana matakin mataimakin alkalin wasa na bidiyo (VAR) na ba da ƙwallon da Newcastle ta ci a matsayin "abin kunya" da kuma "abin takaici".
Sai da aka binciki ƙwallon da Anthony Gordon a kan matakai uku, kafin aka bada cin.
An duba don ganin ko ƙwallon ta fita daga wasa, ko idan an yi ƙeta, ko kuma idan akwai satar gida.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta FA ta fitar ta ce ana zargin Arteta da furta kalaman cin mutunci ga jami'an wasan.
Arteta yana da har zuwa ranar Talata domin amsa tuhumar.
Arsenal ta goyi bayan kalaman Arteta a wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, yayin da kocin ya ce "hakkinsa" ne ya kare ta.