BBC Hausa of Tuesday, 1 August 2023
Source: BBC
Ɗan wasan Brazil Fabinho ya kammala koma wa ƙungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya daga Liverpool a kan kwantiragin shekara uku.
Dan wasan mai shekara 29, bai tafi tare da tawagar ‘yan wasan Liverpool zuwa sansanin horo na baya-bayan nan a ƙasar Jamus ba, bayan tayin da Al-Ittihad ta yi masa na fam miliyan 40.
Haka kuma Fabinho ya fice daga tafiyar da ƙungiyar ke yi a ƙasar Singapore yayin da aka kammala gudanar da cinikin.
Fabinho shi ne babban ɗan wasa na baya-bayan nan da Al-Ittihad ta ɗauka cikin ‘yan wasan da ke kwarara zuwa Gasar Saudi Pro League.
Wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or, kuma tsohon ɗan wasan Real Madrid Karim Benzema da tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea N'Golo Kante da tsohon dan wasan Celtic Jota duk sun koma ƙungiyar da tsohon kocin Spurs da Wolves Nuno Espirito Santo ke horaswa.
Al-Ittihad ta ce ta ɗauko Fabinho ne a ƙoƙarinta na ƙarfafa ayarin kulob ɗin da fitattun ‘yan wasa, waɗanda za su taimaka wajen inganta ƙungiyar, su kuma ba ta damar lashe gasanni a cikin gida da kuma ƙetare.