You are here: HomeAfricaBBC2023 08 14Article 1824806

BBC Hausa of Monday, 14 August 2023

    

Source: BBC

Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12 - MDD

Hoton alama Hoton alama

Farashin abinci a duniya kamar su shinkafa da man kayan gwari zai yi tashin da bai tabayi ba cikin shekara 12.

Wannan na cikin wani rahoto da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fiyar a wannan watan na Agusta, wanda ta ce hakan ya biyo bayan ficewar Rasha ne daga yarjejeniyar fitar da abinci da aka cimma tsakaninta da Ukraine ta ruwa.

FAO ta ce alƙalumanta sun nuna an samu ƙaruwar kashi 12.1 na farashin Man kayan gwari bayan irin wannan tashin da aka samu cikin watanni bakwai a jere.

Farashin shinkafa ma ya tashi da kashi 1.3 a watan Yuli idan aka kwatanta da watan Yuni, kamar yadda FAO ta bayyana a ranar Juma’a.

An riƙa samun faɗuwar kayayyakin abinci a duniya a bara wayan wani tashin gwauron zabi da abincin ya yi lokacin da ake tsaka da rikicin Rasha.

Ƙara samun katsewar fitar da abinci daga da aka samu a bayan nan bayan ficewar Rasha daga cikin yarjejeniyar fitar da abinci da aka cimma da Ukraine, ya sanya ƙayan abinci tashi a faɗin duniya.

Ƙasashen Rasha da Ukraine ne ke kan gaba wajen noma tare da fitar da alƙama da wasu sauran nau’o’in hatsi da akan iya sarrafawa a fitar da su duniya, musamman zuwa nahiyar Afrika da Gabas ta tsakiya da kuma Asiya inda miliyoyin mutane ke fama yunwa.

“Ƙasashen da suka dogara da shigo da abinci za su yi matuƙar kaɗuwa ta tashin farashin, saboda zai janyo hauhawar farashin sauran kayayyaki da talauci da matsalar abinci,” in ji rahoton.

Rashin amfani da Baharul Aswad wajen fitar da hatsi ya janyo tashin farashin alƙama da kashi 1.6 a watan Yuli idan aka kwatanta da wata Yuni.

Rahoton hukumar ya ce wani abu da zai ƙara tayar da hankalin duniya shi ne haramcin fitar da shinkafa da India ta yi, wanda ya sanya ‘yan kasuwar ƙasar ɓoye wadda suke da ita a hannu zuwa kasuwannin duniya.

Haramcin fitar da shinkafa daga Indiya da kuma ficewar Rasha daga yarjejeniyarta da Ukraine ya sanya farashin shinkafa ya tashi da kashi 2.8 a watan Yuli, ya kuma ƙaru da kashi 19.7 a wannan shekarar, mafi yawa tun Satumbar 2011, in ji FAO

Wannan lamari sai ya fi shafar ƙasashen da ke yankin Kudu da Hamadar Sahara saboda su ne suka fi sayo shinkafa daga waje.

Sharhi

Wani abu da zai ƙara ta'azzara matsalar abinci a nahiyar Afrika shi ne rikicin da Nijar ta faɗa da takunkuman da ECOWAS ta ƙaƙaba mata.

Wani rahoton bankin duniya da ya fita a farkon shekarar nan, ya nuna yadda tattalin arziƙin Nijar ke bunƙasa cikin gaggawa, saboda ita ce ƙasa ta biyu bayan Najeriya da take iya fitar da tsaba mai yawa.

A makon jiya sai da wasu al'ummar jihar Sokoto da BBC ta zanta da su suka bayyana yadda suka fara fuskantar tsadar kayan abinci, duk da cewa suna zaune ne a iyakar Najeriya da Nijar.

Wani rahoto da BBC ya yi a makon jiya shi ma ya yi bayanin yadda aka fara samun matsalar albasa a Ghana, inda buhunta ya haura sidi dubu 100, kwatankwacin naira dubu 80.

Read full article