BBC Hausa of Tuesday, 22 August 2023
Source: BBC
Gary Neville ya ce yadda Manchester United ta gudanar da binciken Mason Greenwood ya kasance " abin da bai yi kyau ba" kuma ba shi da kwakkwaran jagoranci.
Greenwood, mai shekaru 21, zai bar United din ne bisa yarjejeniyar tsakaninsa da kungiyar bayan wani bincike na cikin gida a watanni shida.
Hakan ya biyo bayan tuhume-tuhumen da ake yi wa dan wasan da suka hada da yunkurin fyade da cin zarafi a watan Fabrairu.
Da yake magana a shirin Sky Sports Monday Night Football, Neville, mai shekaru 48, wanda ya buga wasa 602 a United, ya kara da cewa: "Matakin da aka bi na yanke hukuncin ba su yi kyau[, idan ana fuskantar manya lamura masu sarkakiya irin wannan na bukatar ingantacen jagoranci, wannan kuma daga kololuwa ake samunsa, Manchester United bata da wannan.'
An kama Greenwood a watan Janairun 2022, sakamakon zarge-zargen da ke tattare da abubuwan da ya wallafa a intanet.
A cikin wata sanarwa, Greenwood ya yarda cewa ya "yi kuskure" amma ya kara da cewa, bai aikata abubuwan da ake zarginsa da su ba.