You are here: HomeAfricaBBC2021 10 01Article 1369972

BBC Hausa of Friday, 1 October 2021

    

Source: BBC

Ghana: Za a rushe sansanin 'yan gudun hijra na Buduburam

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

Gwamnatin kasar Ghana za ta fara rushe matsugunnin 'yan gudun hijira na Liberia Camp ko kuma Buduburam da ke jihar tsakiyar kasar.

Gwamnatin Ghanar ta ce za a rushe sansanin ne domin samar da kyakkyawan tsari ta hanyar gina makarantu da asibitoci da hanyoyi da sauran su.

Sansanin shi ne mafi girma a Ghana, wanda aka kafa shi a shekarar 1990 sanadiyyar barkewar yakin basasa a kasar Liberia, da wanda ya barke na biyu a 1996, wanda ya tilastawa gwamnatin Ghana bai wa `yan gudun hijirar mafaka bayan sun tsere daga can, akwai kuma 'yan gudun hijrar Saliyo da aka ba su mafaka a sansanin.

Sai dai a halin da ake ciki mazauna sansanin sun nuna rashin jin dadi ga wannan aikin da gwamnatin Ghanar ta ce za ta yi ta hanyar zamanantar da shi da ababen more rayuwa.

A ziyarar da wakilin BBC a Ghana Muhammad Fahad Adam ya kai, ya zanta da wasu daga cikin mazauna sansanin Buduburam, wadanda a lokacin da ya kai ziyarar suke hada kayansu, wasu a cikin motoci wasu ma aka suke daukar kayansu domin ficewa.

Yawancin aikin rusau irin wannan da gwamnati ke yi, ta kan tanadi wasu kudade na diyya ga wadanda lamarin zai shafa.

Sai dai wani mazaunin sansanin Buduburam, ya shaida wa wakilin BBC cewa, ba bu wani abu da aka basu, ''Ba bu abin da aka ba mu ko da kuwa takarda ce, gwamnatin da muka zaba ta samu mulki ba ta ma na komai ba".

An ce za a ba mu fili amma har yanzu ba bu abin da muka gani, sannan ba bu tabbacin ko za a dawo da mu idan an kammala gyaran, hasalima ba bu ko wa daga bangaren gwamnati da ya yi magana da mu.

Wadanda suke da dakuna ma an rusa su, kuma ba bu wanda ya zo ya ba mu hakuri.''

Ita ma Mansura Vivian, 'yar gudun hijira ce da ke zaune a sansanin, ta ce tun a shekarar 1999 ta ke sansanin, bayan ta tsero daga Laberiya, kuma ba ta da katin shaida saboda Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta kawo musu amma shiru ba a kawo ba.

Anan inda ta ke 'ya'yanta hudu ba ta san yadda za ta yi ba, sai dai idan an kore su, ta koma gefen titi da zama ita da 'ya'yanta.

Read full article