BBC Hausa of Monday, 5 June 2023
Source: BBC
Pep Guardiola na fatan Ilkay Gundogan zai saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Manchester City.
Kwantiragin dan wasan zai kare a karshen kakar bana, wanda ya ci kwallo biyun da ya bai wa City damar lashe FA Cup ranar Asabar.
City ta yi nasarar lashe kofin bayan cin Manchester United 2-1 a Wembley, kofi na biyu da ta dauka bayan ta lashe Premier League.
City za ta buga wasan karshe a Champions League da Inter Milan, kuma watakila shi ne wasan karshe da zai buga wa kungiyar ta Etihad.
Guardiola da Gundogan sun kulla alaka mai karfi a tsakaninsu, kuma shi ne dan wasan farko da kociyan ya fara dauka a 2016.
Ke nan Gurdiola da Gundogan sun dauki kofi 11 tare, yayin da 'yan wasa suka zabi Gundogan kyaftin din kungiyar, bayan da Fernandinho ya yi ritaya a bara.
Gundogan dan kasar Jamus, ya ci kwallo biyu daga ukun da City ta ci Aston Villa a wasan karshe a bara a Premier League.
Haka kuma ya zama na farko da ya ci kwallo a ƙanƙanin lokaci a FA Cup, wadda ya fara cin Manchester United a dakika 13 da fara tamaula.