BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023
Source: BBC
Akwai yiwuwar dan wasan Manchester City Ilkay Gundogan, mai shekara 32, zai koma Borussia Dortmund a kakan bana, a yayin da Bercelona kuma ba zata iya biyan dan wasan tsakiyar na Jamus albashi ba a yayin da kwantiraginsa zai kare. ( Bild-in German)
Bercelona ta na kokarin shawo kan Gundogan ta hanyar tsawaita kwantiraginsa da shekara uku tare da rage masa albashi, yayin da Arsenal kuma ta yi masa tayin kwantiragin shekara biyu, sannan kuma ana kyautata masa samun tayi mai gwabi daga kungiyar Saudiyya. ( Sport – in Spanish)
Tayin farko da kungiyar Real Madrid zata yi wa Harry Kane zai kasance yuro miliyan 80, to amma Tottenham tun da farko ta taya dan wasan na Ingila a kan yuro miliyan 120. ( Sport – Spanish)
Paris St-German, ta doke Chelsea wajen daukar dan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte, mai shekara 22 daga Sporting Lisbon. ( L’ Equipe – in French)
Chelsea ta rasa damarta ta daukar dan wasan tsakiya na Brighton Moises Caicedo, mai shekaru 21, bayan rasa Ugarte. ( Standard)
Chelsea ta sake nuna sha’awarta kan dan wasan Southampton Romeo Lavia, mai shekaru 19. ( Express)
Alexis Mac Allister, zai koma Liverpool daga Brighton, to amma sai ya gama jinya. (Guardian)
Atletico Madrid na duba yiwuwar daukar Wilfried Zaha. Dan wasan dan kasar Ivory Coast mai shekara 30, zai zamo ba shi da kungiyar da zai bugawa wasa idan har ya ki amincewa da sabuwar kwantiragi a Crystal Palace. ( Mail)
Liverpool, na son biyan Barcelona yuro miliyan 35 domin daukar dan wasan tsakiya na Ivory Coast Franck Kessie, mai shekara 26. ( Sport – in Spanish)