You are here: HomeAfricaBBC2021 06 23Article 1292953

BBC Hausa of Wednesday, 23 June 2021

    

Source: BBC

Gwamnatin jihar Kano ta rufe asibitin yara

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta rufe ayyukan asibitin yara dake titin gida Zoo a Kano bayan shafe kusan shekaru uku da fara aiki.

Matakin gwamnatin na Kano ya dai kawo tsaiko wajen harkokin duba marasa lafiya, sakamakon yadda ma'aikatan asibitin suka gaza sanin makomarsu yayin da marasa lafiya ke kokawa.

Abokin aikin mu a Kano Khalifa Shehu Dokaji da ya ziyarci asibitin yara na Isyaka Rabi'u da ke hanyar gidan adana namun daji, ya ce a sabanin yadda asibitin ke cika makil da marasa lafiya da koke-koken yara, a yanzu shiru ka ke ji.

Wasu daga cikin marasa lafiya da ke jiyya da kuma ba a sallamesu daga asibitin ba, sun yi tagumi suna tunanin a makomar rayuwa, sakamakon fargabar halin da za su shiga idan likitoci da malaman jinya suka daina zuwa aiki.

A cewar daya daga cikin jagororin asibitin da ya nemi a sakaya sunan sa, yace suna tsaka da yin aiki ne sai suka sami wani Umarnin kotu ce na cewar kamfanin dake kula da ayyukan wannan Asibiti mai suna Northfield Health Services ya ba da umarnin kwashe kayansu daga asisbitin tare da ma'aikatan sa baki daya.

''Ba mu san makomar mu ba, saboda babu wani bayani da akai mana, wadanda ke kula da asibiti da shugabannin asibitin ne suka samu sabani, don haka sai an warware matsalar.''

Sai dai shugaban hukumar dake kula da asibitoci a Kano, Dr Nasiru Kabo ya shaidawa BBC cewar gwamatin Kano ba ta rufe asibitin ba, amma ta janye yarjejeniyar kawancen aiki tsakanin ta da Kamfanin Northfield Health Services saboda rashin gamsuwa da yadda yake kula da asibitin.

Bai dai yi karin bayani dangane da inda aka sami umarnin kotun ba tare da yin cikakken bayani kan makomar asibitin. A shekara ta 2018 ne Asibitin yaran na Kano mai yawan gadaje 200 da ake yiwa lakabi da

Read full article