BBC Hausa of Sunday, 14 May 2023
Source: BBC
An sanar da ɗan kwallon Manchester City, Erling Haaland a matsayin gwarzon ɗan kwallon kafa na bana wanda ƙungiyar marubuta ƙwallon ƙafa ta Ingila ke bayarwa.
Haaland ya haskaka sosai a kakar wasa ta bana inda kawo yanzu ya zura kwallo 51 a duka gasar da ya buga.
Rawar da ya taka ta taimaka wa tawagar Pep Guardiola kai wa mataki na farko a teburin gasar firemiyar Ingila da kuma kai wa matakin kusa da ƙarshe a gasar zakarun Turai.
Haaland mai shekaru 22 ya samu kashi 82 cikin 100 na ƙuri'ar da aka kaɗa domin bayar da kyautar.
Ƴan wasan Arsenal Bukayo Saka da kuma Martin Odegaard su ne suka yi na biyu da na uku, sai kuma Kevin De Bruyne ya zo na huɗu a yayin da dan kwallon Manchester United Marcus Rashford ya kasance na biyar.
A ɓangaren mata, 'yar kwallon Chelsea Sam Kerr ce ta samu kyautar a karo na biyu a jere.